"Ni Ne Sila": Tsohon Gwamna da Ya Fice a PDP Ya Magantu Bayan Jiga jiganta Sun Watse

"Ni Ne Sila": Tsohon Gwamna da Ya Fice a PDP Ya Magantu Bayan Jiga jiganta Sun Watse

  • Da alamu tsohon gwamnan Imo, Emeka Ihedioha ya yi wa jam'iyyar PDP illa a jihar tun bayan ficewarsa a kwanakin baya
  • Ihedioha ya bayyana yadda jiga-jigan PDP ke watsar da ita da cewa sun yi imani da salon shugabancinsa ne a jihar
  • Wannan na zuwa ne bayan tsohon gwamnan ya yi murabus daga jam'iyyar wanda ya jawo ficewar jiga-jiganta a jihar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Imo - Tsohon gwamnan jihar Imo, Hon. Emeka Ihedioha ya bayyyana irin shugabancin da ya gudanar a jihar.

Ihedioha ya ce yadda jiga-jigan jam'iyyar PDP ke watse mata ya tabbatar da sun gamsu da shugabancinsa.

Tsohon gwamna da ya bar PDP ya bugi kirji kan shugabancinsa
Tsohon gwamnan Imo, Emeka Ihedioha ya ce ficewarsa a PDP ya nakasa jami'yyar. Hoto: Emeka Ihedioha.
Asali: Twitter

Musabbabin barin Ihedioha jami'yyar PDP

Kara karanta wannan

Badakalar N80bn: Abin da wasu tsofaffin gwamnoni ke cewa game da Yahaya Bello

Ya ce musabbabin barin jami'yyar ya samo asali ne bayan magoya bayansa sun bukaci ya sauya tafiya domin kawo gyara a Imo, cewar Tribune.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon mataimakin kakakin Majalisar Tarayya ya zargi jami'yyar a matakin jiha da kasa da rashin kawo sauyi ga PDP.

Ihedioha ya koka kan yadda jami'yyar ta gagara yin katabus a zaben da aka gudanar a kasar baki daya, cewar Independent.

Ihedioha ya bayyana yadda PDP ta lalace

Ihedioha ya ce mutane da dama sun dawo daga rakiyar cewa jam'iyyar za ta sake yin wani abin kirki.

Wannan na zuwa ne bayan tsohon gwamnan ya watsar da jam'iyyar inda ya yi murabus duk da kasancewa daga cikin wadanda suka rene ta a jihar tun 1998.

Bayan yin murabus din Ihedioha, jiga-jigan jami'yyar da dama sun yi fatali da ita wadanda suka nuna goyon bayansu ga tsohon gwamnan.

Kara karanta wannan

Jigon PDP ya 'fallasa' babban dalilin rikicin Nyesom Wike da sabon Gwamnan Ribas

Shema ya bar jam'iyyar PDP a Katsina

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Katsina, Barista Ibrahim Shema ya yi fatali da jam'iyyar PDP a jihar.

Shehu Shema ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC ne a jiya Alhamis 2 ga watan Mayu a gundumar Shema da ke karamar hukumar Dutsin-Ma.

Tun a watan Agustan 2023 ne aka gano Shema ya kai wa shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ziyara a kokarin barin PDP.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.