Tsohon Gwamnan Katsina Ya Watsar da PDP, Ya Rungumi APC Mai Mulki
- Tsohon gwamnan jihar Katsina, Barista Shehu Shema ya watsar da kashin jami'yyar PDP mai adawa a jihar
- Tsohon gwamnan ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a yau Alhamis 2 ga watan Afrilu a karamar hukumar Dutsin-Ma
- Jiga-jigan jam'iyyar APC da mukarraban gwamnati da dama sun halarci taron sauya shekar na tsohon gwamna, Shema
Abdullah Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Katsina - Tsohon gwamnan jihar Katsina, Barista Ibrahim Shehu Shema ya koma jam'iyyar APC.
Shema ya sauya sheka a yau Alhamis 2 ga watan bayan ga watsar da jam'iyyar PDP mai adawa a jihar.
Yaushe Shema ya gana da Ganduje?
Tun a watan Agustan shekarar 2023 ne Shema ya yi wata ganawa da shugaban APC, Abdullahi Ganduje kan komawa jami'yyar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan ya goyi bayan Atiku Abubakar a zaɓen shugaban kasa amma a matakin jiha ya yi jam'iyyar APC inda Dikko Umar Radda ya sanu nasara.
Gwamna Dikko Umar Radda ne ya karɓi tsohon gwamnan tare da jiga-jigan jam’iyyar APC a karamar hukumar Dutsinma da ke jihar.
Na hannun daman Shema sun koma APC
Kafin sauya shekar tsohon gwamnan, ya turo wasu na hannun damansa da suka koma jam’iyyar APC, lamarin da ya jefa shakku kan kasancewarsa jam'iyyar PDP.
Shugaban jam'iyyar APC a jihar da Hon. Hamisu Gambo (Dan-Lawan Katsina) sun halarci taron sauya shekar tsohon gwamnan a karamar hukumar Dutsin-Ma.
Daga bisani wadanda suka wakilci tsohon gwamnan sun karba masa katin zama ɗan jam'iyyar a gundumar Shema da ke karamar hukumar Dutsin-Ma.
Tsohon gwamnan Imo ya watsar da PDP
A wani labarin, tsohon gwamnan jihar Imo, Honarabul Emeka Ihedioha, ya fice daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).
Ihedioha ya bayyana cewa PDP ta gaza warware matsalolinta na cikin gida ko aiwatar da dokokinta da kuma gaza yin sahihiyar adawa ga jam’iyyar APC.
Murabus din nasa na zuwa ne kwanaki kadan bayan da jam’iyyar PDP ta gudanar da taron kwamitin zartarwa na kasa (NEC).
Asali: Legit.ng