Jiga Jigan APC 5 da Ake Zaton Za Su Raba Gari da Tinubu a Zaben 2027
Bisa ga dukkan alamu shugaban kasa, Bola Tinubu ya samu matsala da wasu jiga-jigan jam'iyyar APC da suka bashi gudunmawa a zaɓen 2023.
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Akwai wasu manyan 'yan siyasa da suka yi ruwa da tsaki wurin tabbatar da nasarar Bola Tinubu a zaben 2023, amma yanzu ba a jin ɗuriyarsu tun bayan hawan shugaban mulki.
Tinubu zai iya fuskantar matsala a 2027
Ana jita-jitar cewa watakila wasu daga cikin 'yan siyasar ba za su goyi bayansa ba a zaben 2027 mai zuwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit Hausa ta jero muku manyan 'yan siyasa da ake zato sun raba gari da shi.
1. Nasir El-Rufai
Akwa alamun alaka ta yi tsami tsakanin tsohon gwamna, Nasir El-Rufai da gwamnatin Bola Tinubu tun bayan kin amincewa da shi a matsayin Minista.
Tun bayan wannan lokaci El-Rufai ke sukar gwamnatin Tinubu musamman ta bangaren cire tallafin man fetur.
Wasu masu fashin baki suna ganin zai yi wahala El-Rufai da Tinubu su yi aiki tare a zaben 2027 kamar yadda suka yi a 2023.
2. Yahaya Bello
Dambarwar da ke tsakanin Yahaya Bello da hukumar EFCC kadai ya isa mutum ya tabbatar akwai matsala a tsakaninsa da Tinubu.
Hakan ya tabbatar da rashin samun goyon bayan gwamnati bayan Ministan Shari'a, Lateef Fagbemi ya bukace shi da ya mika kansa.
3. Femi Fani-Kayode
Kakakin kamfe na shugaban kasa, Fani-Kayode shi ma akwai alamun ba ya jituwa da gwamnatin Bola Tinubu.
Yanzu kusan shekara da kafa gwamnati amma babu wani mukami da tsohon Ministan ya samu daga Tinubu, cewar Africa Report.
Abin da ya fi ba da mamaki shi ne fitar da sunayen Ministoci kashi na farko da na biyu ba tare da sunan Fani-Kayode ba.
4. Kayode Fayemi
Tsohon gwamn jihar Ekiti, Kayode Fayemi na daga cikin 'yan takarar shugaban kasa da suka janyewa Tinubu a zaben fidda gwani, cewar PM News.
'Yan Najeriya da dama sun yi tsammanin kasancewar Fayemi a gwamnatin Tinubu amma har yanzu shiru kake ji.
5. Ibikunle Amosun
Tsohon gwamnan Ogun, Ibikunle Amosun shi ma ya janyewa Tinubu takara a zaben fidda gwani gabanin zaben 2023..
Amosun ya ƙi neman zarcewa a matsayin sanata saboda kudirin neman shugabancin kasar.
Bayan rasa damar komawa kujerar sanata, har yanzu Amosun bai samu damar kasancewa cikin gwamnatin Tinubu ba.
'Yan siyasa da suka buga da ƴaƴansu
Kun ji cewa a Najeriya akwai wasu manyan 'yan siyasa da suka samu matsala da ƴaƴansu ko iyalansu kan siyasa.
A wannan rahoto, Legit Hausa ta jero muku fitattun 'yan siyasa da suka yi fito-na-fito da ƴaƴansu saboda bambancin ra'ayi.
Asali: Legit.ng