Shugaban APC Ganduje Ya Caccaki Jiga Jigan NNPP, Ya Faɗi Tuggun da Aka 'Shirya' Masa

Shugaban APC Ganduje Ya Caccaki Jiga Jigan NNPP, Ya Faɗi Tuggun da Aka 'Shirya' Masa

  • Dakta Abdullahi Ganduje ya soki shugabannin NNPP inda ya zarge su da shirya makircin tsige shi daga shugabanncin APC
  • Shugaban na APC na kasa ya bayyana jagororin NNPP a matsayin waɗanda ta kare masu a fagen siyasa kuma duk sun gaza
  • Ya ce duk da suna hangen kujerar shugaban ƙasa a 2027 amma sama ta yi wa zabo nisa domin Tinubu zai yi tazarce zango na biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana New Nigeria Peoples Party (NNPP) a matsayin jam’iyyar ‘yan siyasar da suka gaza.

Ganduje, tsohon gwamnan jihar Kano ya faɗi haka ne yayin jawabi ga gamayyar ƙungiyoyin magoya baya, waɗanda suka kai masa ziyara a hedkwatar APC da ke Abuja.

Kara karanta wannan

Malam El-Rufai zai kara da Tinubu a zaben shugaban ƙasa a 2027? Gaskiya ta bayyana

Shugaban APC, Abdullahi Ganduje.
Ganduje ya bayyana Kwankwaso da sauran jiga-jigan NNPP a matsayin ƴan siysar da suka gaza Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Ganduje ya tabo ƙusoshin NNPP

Ganduje ya zargi jiga-jigan NNPP da ƙulla makircin zanga-zanga a wani yunƙuri na raba shi da kujerar shugaban APC na ƙasa, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce wasu jiga-jigan jam’iyyar NNPP na kwaɗayi da hangen kujerar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.

Amma a cewarsa, ba za su samu ba saboda shugaban ƙasar zai nemi tazarce a zaɓe na gaba kuma babu tantama zai zarce wa'adi na biyu a kujerar mulkin Najeriya.

Jiga-Jigan NNPP sun firgita

A ruwayar The Nation, Ganduje ya ce:

"Sun firgita saboda muna ƙara karfi, sun tsorata saboda duk inda suka waiga a faɗin ƙasar nan muke karɓan sababbin mambobi zuwa cikin jam'iyyar mu, hakan ya firgita su.
"Suna hangen 2027 amma babu wuri a wannan lokacin, shugaban kasar mu, Bola Ahmed Tinubu ne in Allah ya so zai ci gaba da jan ragamar Najeriya.

Kara karanta wannan

Edo: Babban jigon APC ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP ana shirin zaɓen gwamna

Ganduje ya buƙaci dukkan mambobin jam'iyyar APC su yi kunnen uwar shegu da dakatarwan da aka masa wadda ya bayyana a matsayin wasan kwaikwayon Afrika Magic.

“Don haka muna rokon ku da ku jajirce wajen ganin jam’iyyarmu ta samu ci gaba," in ji shi.

- Abdullahi Ganduje

Sakamakon JAMB ya fito

A wani rahoton kuma Sakamakon jarabawar share fagen shiga manyan makarantun gaba da sakandire (UTME) wanda ɗalibai suka kammala ya fita

Hukumar da ke da alhakin shirya jarabawar (JAMB) ce ta bayyana sakin sakamakon ɗalibai miliyan 1.94 da suka zana jarabawar a bana 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262