Yana Cikin Rikici da Wike, Gwamna Fubara Ya Sha Sabon Alwashi
- Gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara, ya sha alwashin cewa ba zai mulki jihar ba ta hanyar durƙusawa wani
- Gwamna Fubara ya kuma buƙaci duk masu son ci gaban jihar da su zo su bada goyon baya domin a ceto ta
- Ya yi jawabi ne dai a lokacin da ya je ta'aziyya a gidan tsohon gwamnan jihar, Celestine Omehia, wanda mahaifiyarsa ta rasu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Ribas - Gwamna Siminalayi Fubara, na jihar Ribas ya sha alwashin cewa ba zai mulki jihar ta hanyar durƙusawa wani ba.
Gwamnan ya yi alƙawarin kare ruhin jihar mai arziƙin man fetur wacce take a shiyyar Kudu maso Kudu.
Fubara, wanda a halin yanzu yana cikin rikicin siyasa tare da magabacinsa kuma ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya roƙi goyon bayan duk ƴan asalin jihar domin ceto ta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya yi magana ne a ranar Asabar, 27 ga Afrilu, a gidan tsohon gwamnan jihar, Celestine Omehia, a ƙaramar hukumar Ikwerre, cewar rahoton jaridar The Nation.
Fubara, tare da rakiyar wasu dattawan jihar, sun kai ziyarar ta'aziyya ga Celestine Omehia bisa rasuwar mahaifiyarsa, Ezinne Cecilia Omehia.
Gwamnan na Ribas ya bayyana cewa ya kai ziyarar ne domin yin ta'aziyya ga tsohon gwamnan.
Wane alwashi Gwamna Fubara ya yi?
Ya kuma jaddada buƙatar kowane mai son jihar ya tashi tsaye domin ya shiga a dama da shi wajen ceto ta, rahoton Daily Post ya tabbatar.
"Duk wanda ya ce yana son jihar nan, kada ya kasance cikin wani abu kai tsaye ko a kaikaice, wanda zai kawo mana koma baya."
"Za mu ci gaba da bayar da goyon baya ga duk abin da zai ɗaga darajar muradun jiharmu ta Ribas."
"Sannan ina farin cikin cewa, sannan na sha faɗi ba sau ɗaya ba sau biyu ba, ban damu da yawan mutanen da ke tare da ni ba, zan tsaya a ɓangaren gaskiya."
"Ba zan yi ba, na sake maimaitawa, ba zan mulki jihar nan gwiwoyina a durƙushe ba."
- Siminalayi Fubara
Kwamishinonin Fubara sun ajiye aiki
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu kwamishinoni guda huɗu na jihar Ribas sun ajiye aikin da Gwamna Siminalayi Fubara ya naɗa su.
Kwamishinonin da suka ajiye aikin sun haɗa da kwamishinan ayyuka George Kelly, kwamishinan wutar lantarki Henry Ogiri, kwamishinan shari'a Farfesa Zacchaeus Adango da kwamishinan kuɗi Isaac Kamalu.
Asali: Legit.ng