Edo: Babban Jigon APC Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar PDP Ana Shirin Zaɓen Gwamna

Edo: Babban Jigon APC Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar PDP Ana Shirin Zaɓen Gwamna

  • Jigon APC a jihar Edo ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP yayin da ake shirin zaɓen gwamna a watan Satumba mai zuwa
  • Honorabul Ogini Kingsley Topa ya bayyana cewa ya ɗauki wannan matakin ne domin marawa Gwamna Obaseki baya a ƙoƙarinsa na kawo ci gaba
  • Ya kuma yaba da naɗin ɗan yankinsa a matsayin mataimakin gwamna, inda ya ce gwamnan ya nuna bai manta da su ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Edo - Jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ta rasa babban jigo wanda ya yi fice wajen haɗa magoya baya tun daga tushe a ƙaramar hukumar Akoko-Edo ta jihar Edo.

Homorabul Ogini Kingsley Topa ya sauya sheƙa daga APC zuwa Peoples Democratic Party (PDP) yayin da ake shirye-shiryen zaɓen gwamna a watan Satumba.

Kara karanta wannan

Zaben Ondo: Jigon APC ya hango rashin nasara ga jam'iyya, ya bayyana dalili

APC da PDP.
Jigon APC ga hakura da zama inuwar tsintsiya, ya koma PDP a jihar Edo Hoto: Official PDP, APC
Asali: Facebook

Topa, wanda aka fi sani da ‘Gwamna lamba 1’ ya taba riƙe muƙamin shugaban kwamitin ayyuka da gidaje a karamar hukumar Akoko-Edo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa Topa ya koma PDP?

'Dan siyasar ya ce ya bar jam’iyyar adawa watau APC zuwa PDP ne domin ya marawa ƙoƙarin Gwamna Godwin Obaseki baya domin kawo ci gaba a jihar, rahoton Leadership.

Fitaccen ɗan siyasar ya kuma yabawa Gwamna Obaseki bisa naɗin Marvellous Omobayo, ɗan salin yankin Akoko-Edu a matsayin mataimakin gwamna, cewar Independent.

A cewarsa, wannan babbar alama ce da ke nuna kaunar da Gwamna Obaseki ke yi wa al'ummarsa Akoko-Edu, wadda a baya ake nuna mata wariya duk da tafi ko wane yankin yawa.

Ya ce:

"Lokaci ya yi da zamu jingine siyasar jam'iyya mu ɗauki siyasar kawo wa al'umma ci gaba domin kowa ya amfana."

Kara karanta wannan

Ana cikin nemansa Yahaya Bello ya kalubalanci hukumar EFCC

"Eh ina APC amma duba da abin da Gwamna Obaseki ya yi wa mutanen Akoko-Edo na naɗa ɗaya daga cikin ƴaƴanmu a kujerar mataimakin gwamna, ya shiga zuƙatanmu kuma ya kafa tarihi.
"Muna matuƙar farin ciki da wannan naɗi wanda ya nuna mana cewa ba a manta da mu ba."

IGP ya janye ƴan sanda daga PCACC

A wani rahoton kuma babban sufetan ƴan sanda na ƙasa (IGP), Kayode Egbetokun ya janye jami'an ƴan sanda daga hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Kano

A cewar wata majiya daga hukumar, ƴan sandan da aka ɗauke suna taimakawa a manyan bincike ciki har da na shugaban APC, Abdullahi Ganduje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262