PDP Ta Sake Samun Naƙasu Bayan Tsohon Gwamna Ya Yi Murabus, an Rasa Jiga-jigai 8
- Jiga-jigan jam'iyyar PDP akalla guda takawa ne suka watsar da lema a jihar Imo a yau Laraba 24 ga watan Afrilun 2024
- Jam'iyyar ta samu naƙasun ne bayan tsohon mataimakin kakakin Majalisar Tarayya, Emeka Ihedioha ya yi murabus
- Emeka ya ce ya bar jam'iyyar ce saboda rashin katabus wurin yin adawa mai karfi ga jam'iyya mai mulki ta APC a Najeriya
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Imo - Jami'yyar PDP ta sake cin karo da matsaloli a Imo bayan murabus din tsohon gwamnan jihar, Emeka Ihedioha.
Akalla jiga-jigan jam'iyyar PDP takwas ne suka yi murabus domin bin sahun tsohon gwamnan jihar.
Su waye suka watsar da PDP a Imo?
Daga cikin wadanda suka yi murabus din akwai mai ba da shawara ga PDP a jihar kan shari'a, Kissinger Ikeokwu da sakataren yada labarants, Emenike Nmeregini da ma'ajin jam'iyyar, David Abanihi, a cewar The Cable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran sun hada Obioma Iheduru da Nwokeke Chukwuemeka da Stanley Okezie da sauran jiga-jigan jam'iyyar da suka ba da muhimmiyar gudunmawa.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da suka tura zuwa ga shugabannin jam'iyyar a gundumominsu da ke jihar.
Matsalolin da PDP ke fuskanta a Najeriya
Wannan na zuwa ne bayan jam'iyyar ta kasa ta shiga rudani kan rikicin shugabanci da ya dabaibaye ta, cewar rahoton Nigerian Pilot.
Murabus din jiga-jigan jam'iyyar PDP a Imo na zuwa ne mako daya bayan gudanar da babban taron jam'iyyar na kasa a Abuja.
Kafin gudanar da ganawar, wasu mambobin jam'iyyar sun bukaci shugaban riko na jam'iyyar, Umar Damagun ya yi murabus daga kujerarsa.
Tsohon gwamnan PDP ya yi murabus
A wani labarin, kun ji cewa tsohon mataimakin kakakin Majalisar Wakilai, Emeka Ihedioha ya yi murabus daga jam'iyyar PDP.
Tsohon gwamnan gwnanan jihar Imo a karkashin jam'iyyar ya bayyana murabus din nasa ne a jiya Talata 23 ga watan Afrilu.
Dan siyasar ya ce musabbabin yin murabus din nasa bai rasa nasaba da yadda jam'iyyar ta gaza yin adawa mai karfi a kasar.
Asali: Legit.ng