Daga Karshe Ganduje Ya Bayyana Wadanda Suka Kitsa Dakatar da Shi Daga Jam'iyyar APC

Daga Karshe Ganduje Ya Bayyana Wadanda Suka Kitsa Dakatar da Shi Daga Jam'iyyar APC

  • Daga ƙarshe Abdullahi Umar Ganduje ya yi magana kan batun dakatarwar da aka yi masa a mazaɓarsa a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa ta jihar Kano
  • Ganduje ya ce za a iya kwatanta batun dakatar da shi da wani irin wasan kwaikwayo da ake yi a tashar 'Africa Magic'
  • Shugaban jam’iyyar APC na ƙasan ya yi magana ne a lokacin da ya karɓi baƙuncin wasu jiga-jigan jam’iyyar a Abuja a ranar Talata, 23 ga watan Afrilu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Abdullahi Umar Ganduje, a ranar Talata, 23 ga watan Afrilu, ya ce gwamnatin jihar Kano ce ke da hannu a dakatarwar da aka yi masa daga jam'iyyar APC.

Kara karanta wannan

Masu ruwa da tsaki a APC sun goyi bayan dakatar da Ganduje, sun buƙaci abu 1

Tsohon gwamnan na jihar Kano ya kuma ce babu wani abin da zai ɗauke masa hankali wajen ganin ya mayar da jam'iyyar APC zaɓin talakawan Najeriya.

Ganduje ya zargi gwamnatin Kano
Ganduje ya zargi gwamnatin Kano da kitsa dakatar da shi daga APC Hoto: @OfficialAPCNg
Asali: Twitter

Ya yi nuni da cewa ko kaɗan bai damu da dakatarwar da aka yi masa ba wacce ya zargi gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf da kitsawa, cewar rahoton jaridar The Nation

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jaridar The Punch ta ce Ganduje ya bayyana hakan ne lokacin da yake jawabi a sakatariyar jam’iyyar APC ta ƙasa a Abuja lokacin da ƙungiyar shugabannin jam’iyyar APC na jihohi suka kai masa ziyarar nuna goyon baya.

Wa ya kitsa dakatar da Ganduje?

"Mun yi mamaki lokacin da muka ji labarin dakatarwar, amma ba mu yi mamaki ba lokacin da muka fahimci cewa babbar barazanar da APC ke yi wa sauran jam'iyyu gaskiya ce, kuma jihar Kano ma na ciki."

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta bayyana sahihancin dakatarwar da aka sake yi wa Ganduje

"Gwamnatin jihar Kano ce ke da alhakin wannan wasan kwaikwayon. Hatta wasan kwaikwayon wani irin wasan kwaikwayo ne da ake kira 'Africa Magic'. Wannan 'Africa Magic' ɗin ba zai kai dimokuraɗiyya ko ina ba."

- Abdullahi Umar Ganduje

A halin da ake ciki, shugaban riƙo na ƙungiyar, Cornelius Ojelabi, ya ce sun je sakatariyar jam’iyyar ta ƙasa ne domin tabbatar da goyon bayansu ga tsohon gwamnan na jihar Kano.

Matsayar APC kan dakatar da Ganduje

A wani labarin kuma, kun ji cewa Jam'iyyar APC reshen jihar Kano, ta buƙaci jama’a da su yi watsi da batun dakatar da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Sakataren jam’iyyar a jihar, Alhaji Zakari Sarina, shi ne ya bayyana hakan inda ya ƙara da cewa dakatarwar da aka yi wa tsohon gwamnan na Kano ba ta da amfani.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng