"Ina Son Na Gurfana a Gaban Kotu," Tsohon Gwamna Yahaya Bello Ya Faɗi Abu 1 da Yake Tsoro

"Ina Son Na Gurfana a Gaban Kotu," Tsohon Gwamna Yahaya Bello Ya Faɗi Abu 1 da Yake Tsoro

  • Alhaji Yahaya Bello ya shaidawa babbar kotun tarayya mai zama a Abuja cewa a shirye yake ya gurfana gabanta kan tuhume-tuhumen da ake yi masa
  • Amma tsohon gwamnan ta hannun ɗaya daga cikin lauyoyinsa ya ce abin da ke hana shi zuwa zaman kotun shi ne tsoron EFCC ta cafke shi
  • Lauyan Yahaya Bello ya koka kan cewa an ba da sammacin kama wanda yake karewa tun gabanin a sanar da shi laifukan da ake zarginsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya ce a shirye yake ya gurfana a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Abuja kan tuhume-tuhume 19 da ake zarginsa.

Kara karanta wannan

"Allah kaɗai ke ba da mulki," Atiku ya mayar da martani kan zargin cin amana a taron NEC

Idan ba ku manta ba hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta maka Yahaya Bello a gaban kotu tana tuhumarsa da aikata laifuka 19 na halasta kudin haram.

Yahaya Bello.
EFCC: Yahaya Bello ya bayyana cewa a shirye yake ya gurfana a gaban kotu Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

Amma yayin zaman kotun yau Talata, ɗaya daga cikin lauyoyin tsohon gwamnan, Adeola Adedipe, SAN, ya shaidawa alkali cewa Bello ya shirya kawo kansa kotu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Lauyan ya bayyana cewa wanda yake karewa yana da niyyar bayyana a gaban kotu to amma yana tsoron hukumar EFCC ta cafke shi kuma ta tsare shi a hannun ta.

Yahaya Bello ya faɗi dalilinsa

Kamar yadda The Nation ta ruwaito, Adedipa ya ce:

"Wanda ake ƙara a shirye yake ya halarci zaman kotu amma yana tsoron akwai umarnin damƙe shi da kotun ta bayar."

Ya roki kotun da ta soke umarnin kama tsohon gwamnan da ta yi a baya, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Ganduje na nan a matsayin shugaban APC na ƙasa bayan hukuncin kotu, bayanai sun fito

Adedipe ya bayar da hujjar cewa ba a sanar da Yahaya Bello tuhume-tuhumen da ake yi masa ba kamar yadda doka ta tanada a lokacin da aka bayar da sammacin kama shi.

Lauyan ya ƙara da cewa sai ranar Talata da za a ci gaban da zaman shari'ar ne sannan kotun ta tura takardar tuhumar tsohon gwamnan ta hannun lauyansa.

"Lokacin da aka ba da sammacin kama shi, ba a sanar da shi batun shari'ar ba, sai yau da safe ne saƙon ya iso. Ya kamata kotu ta soke umarnin kama shi kafin mu bar harabar nan," in ji lauyan.

Bayelsa: Kotu ta tanadi hukunci

A wani rahoton kuma kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan jihar Bayelsa ta shirya yanke hukunci a ƙarar da ɗan takarar APC, Timipre Sylva, ya shigar.

Mai shari'a Adekunle Adeleye ya bayyana cewa cikin kwanaki 180 kotu za ta sa rana kuma ta yanke hukunci kamar yadda doka ta tanada.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262