Masu Ruwa da Tsaki a APC Sun Goyi Bayan Dakatar da Ganduje, Sun Buƙaci Abu 1
- Masu ruwa da tsakin jam'iyyar APC sun fara juyawa Ganduje baya kan batun dakatar da shi a gundumarsa da ke jihar Kano
- Wannan na zuwa ne bayan wani tsagin APC a gundumar Ganduje sun sake fitowa sun tabbatar da dakatar da shi a karo na biyu
- Amma jiga-jigan APC a Arewa ta Tsakiya sun bayyana cewa dama kujerar tasu ce, don haka suka roki Tinubu da NEC su maye gurbin da ɗan yankinsu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a yankin Arewa ta Tsakiya sun goyi bayan dakatarwar da aka yi wa shugaban jam’iyyar na kasa, Dakta Abdullahi Ganduje.
Sannan sun buƙaci cewa kujerar shugaban APC na ƙasa wadda Abdullahi Adamu ya riƙe a baya ta koma shiyyarsu watau Arewa ta Tsakiya.
Jiga-Jigan jam'iyya mai mulkin sun bayyana cewa dama tun asuli ƙaƙaba Ganduje aka yi a kujerar shugaban jam'iyya wanda hakan ya saɓa wa tsarin daidaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka dakatar da Ganduje
Wannan kalamani na masu ruwa da tsakin na zuwa ne yayin da wani tsagin APC a gundumar Ganduje da ke Dawakin Tofa a Kano ya sake dakatar da tsohon gwamnan.
Kamar yadda Punch ta ruwaito, tun farko mai ba da shawara kan harkokin shari'a, Haladu Gwanjo, ya jagoranci shugabannin jam'iyyar suka dakatar da Ganduje.
Bayan haka kuma babbar kotun jihar Kano ta tabbatar da wannan ddakatarwa, lamarin da APC ta jiha ta soke nan take kuma ta ɗauki matakin kan shugabannin gunduma.
Bugu da ƙari, babbar kotun tarayya ta jingine wannan dakatarwa, inda ta umarci Ganduje ya ci gaba da zama a kujerar shugaban APC na ƙasa.
Ana cikin tirka-tirka kan haka ne ranar da Lahadi, wani tsagin APC a gundumar Ganduje, wanda ya yi ikirarin shi ne halastacce, ya tabbatar da dakatar da tsohon gwamnan, rahoton Leadership.
Masu ruwa da tsaki sun goyi baya
Da yake mayar da martani a Abuja, wani jagoran masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Arewa ta Tsakiya, Muhammad Etsu, ya ce suna goyon bayan dakatarwar.
Etsu ya kara da cewa dama kuskure ne APC ta maye gurbin tsohon shugaban jam’iyyar, Abdullahi Adamu, wanda ya fito daga yankinsu da Ganduje dan Arewa maso Yamma.
Ya kuma roƙi shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da kwamitin zartaswa na APC ta ƙasa su amince da dakatar da Ganduje, kana su dawo da kujerar yankin Arewa ta Tsakiya.
"Muna kira ga dukkan shugabannin jam’iyyar APC da masu ruwa da tsaki da su marawa kudurin Arewa ta tsakiya baya.
"Hakan zai karawa jam’iyyar karfi, da hadin kai wanda zai share fagen samun ci gaba da faɗaɗa karfin jam'iyya a dukkan sassan ƙasar nan."
- Muhammad Etsu.
Shugaban PDP bai tsira ba
A wani rahoton kuma duk da ya tsallake a taron kwamitin zartaswa NEC, muƙaddashin shugaban PDP ya ci gaba da fuskantar matsin lamba ya yi murabus
Tsohon ɗan majalisar tarayya, Farah Dagogo, ya buƙaci Umar Damagum ya yi murabus matukar yana kishin PDP a zuciyarsa
Asali: Legit.ng