Reno Omokri Ya Wofantar da Obi, Ya Kwantanta Shi da Shugaban Karamar Hukuma
- Reno Omokri, tosohn hadimin Goodluck Jonathan ya caccaki Peter Obi kan rashin tabuka wani abin kirki lokacin da ya ke mulki
- Reno ya kalubalanci magoya bayan Obi da su kawo makaranta daya da tsohon gwamnan ya fara kuma ya kammala a Anambra
- Omokri ya ce shugaban ƙaramar hukumar Eti-Osa a jihar Legas ya fi Peter Obi aiki idan aka kwatanta lokacin da ya ke mulkin jihar Anambra
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Tsohon hadimin Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya sake caccakar dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi.
Omokri ya ce ayyukan da Obi ya yi cikin shekaru takwas a jihar Anambra bai kai ayyukan da ciyaman na karamar hukumar Legas ya yi ba.
Omokri ya kwantanta Obi da ciyaman
Dan takarar shugaban kasar ya mulki jihar Anambra ne daga watan Yunin shekarar 2007 zuwa watan Maris na 2014.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Reno ya bayyana haka ne yayin shirin 'Mic On Podcast' na Channels TV da ya wallafa a shafinsa na Facebook.
"Shugaba karamar hukumar Eti-Osa a jihar Legas ya cimma abubuwa fiye da mulkin Peter Obi."
"Na tabbatar kuma na sani, ciyaman na karamar hukumar Eti-Osa ya gina akalla makarantu uku."
- Reno Omokri
Omokri ya kalubalanci Peter Obi
Omokri ya kalubalanci magoga bayan Peter Obi da ake kira 'Obidients' da su kawo makaranta da ya gina a jihar Anambra.
"Zan ba da kyautar $10,000 ga 'yan Obidents da suka kawo makaranta daya da Obi ya fara ya kuma kammala tare da kaddamarwa."
- Reno Omokri
Har ila yau, tsohon kakakin Jonathan ya musanta cewa Obi ya fi Rabiu Kwankwaso da Shugaba Bola Tinubu.
Jigon APC ya kalubalanci atiku da Obi
A wani labarin, kin ji cewa jigon jami'yyar APC, Bosun Oladele ya caccaki 'yan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar da Peter Obi.
Bosun ya kalubalance su da su lissafo abin da suka tsinana yayin da suke rike da madafun iko a Najeriya.
Tsohon ɗan Majalisar ya yabawa Shugaba Tinubu kan ayyukan da ya ke yi a kasar inda ya ce da kasar na hannun Atiku ko Obi da ta durkushe.
Asali: Legit.ng