Ana Cikin Takaddamar Ganduje, 'Yan APC 1000 Sun Sauya Sheka Zuwa NNPP a Kano
- Jam'iyyar All Progressives Congress ta samu koma baya bayan mambobinta mutum 1000 sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar NNPP
- Masu sauya sheƙar sun samu tarba a gidan gwamnatin jihar inda aka karɓe su a matsayin sababbin ƴan jam'iyya mai mulki a jihar
- Shugaban NNPP na jihar ya yi maraba da shigowar su jam'iyyar inda ya ba su tabbacin cewa za a dama da su
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Sama da mambobin jam’iyyar APC 1,000 a jihar Kano sun sauya sheƙa zuwa jam’iyyar NNPP.
Mataimakin gwamnan jihar, Aminu Gwarzo, shi ne ya karɓi masu sauya sheƙar a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf a hukumance a gidan gwamnati dake Kano, a ranar Asabar, 20 ga watan Afrilu.
Gwarzo ya yi wa kowane daga cikinsu ado da hular Kwankwasiyya, cewar rahoton jaridar The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wata sanarwa da babban sakataren yaɗa labaran mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba, ya fitar, ta ce waɗanda suka sauya sheka sun fito ne daga ƙananan hukumomin Shanono da Bagwai na jihar.
Mataimakin gwamnan ya jaddada cewa jam’iyyar NNPP tana fifita haɗin kai kuma za ta yi wa dukkan ƴaƴanta adalci.
Gwarzo ya jaddada ƙudirin gwamnatin na aiwatar da shirye-shiryen da za su amfana daukacin jihar Kano, ya kuma buƙaci a ci gaba da goyon bayan gwamnatinsu.
Meyasa suka bar APC zuwa NNPP?
Shugaban masu sauya sheƙar, Haruna Abbas, ya ce sun koma NNPP ne saboda halin shugabanci nagari da salon mulkin Gwamna Abba, rahoton jaridar Daily Post ya tabbatar.
Ya nuna nadamarsa kan yadda suka kasance a jam'iyyar APC a baya, sannan ya yi alƙawarin yin tuƙuru da jam'iyyar NNPP domin ci gaban jihar Kano.
Shugaban jam'iyyar NNPP na jihar Kano, Hashimu Dungurawa, ya yi maraba da shigowar su jam'iyyar inda ya ba su tabbacin za a dama da su a cikin harkokin jam'iyyar.
Legit Hausa ta nemi jin ta bakin kakakin jam'iyyar APC na jihar Kano, Ahmed S. Aruwa, kan sauya sheƙar da mambobin na jam'iyyar ta su suka yi zuwa cikin jam'iyya mai mulki a jihar.
Kakakin ya bayyana cewa baya da masaniya kan batun sauya sheƙar da mambobin na APC suka yi.
"Eh gaskiya bani da masaniya kan batun wannan sauya sheƙar amma zan kira shugaban APC na ƙaramar hukumar Bagwai domin tabbatarwa."
Tsagin APC ya sake dakatar da Ganduje
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsagin jam'iyyar APC a matakin unguwa ya sake dakatar da Abdullahi Ganduje a jami'yyar.
Tsagin ya dakatar da tsohon gwamnan ne kan zargin cin dunduniyar jami'yyar da ya jawo mata rashin nasara a zaɓen 2023.
Asali: Legit.ng