Kogi: Gwamna Ya Sake Burmawa Matsala Kan Sulalewa da Yahaya Bello, an Bukaci Tsige Shi

Kogi: Gwamna Ya Sake Burmawa Matsala Kan Sulalewa da Yahaya Bello, an Bukaci Tsige Shi

  • Wani lauya a Najeriya, Deji Ajare ya bukaci Majalisar dokokin jihar Kogi da ta fara shirin tsige gwamnan jihar, Usman Ahmad Ododo
  • Lauyan ya tura wannan bukata ce ta hannun magatakardan Majalisar inda ya ce hakan ya zama dole ganin yadda gwamnan ya saba dokar kasa
  • Ajare ya ce gwamnan ya kawo cikas ga bangaren shari'a yayin da ya yi amfani da karfin mulkinsa wurin sulalewa da tsohon Gwamna, Yahaya Bello

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Yayin da ake ci gaba da neman tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, Gwamna Usman Ododo ya shiga cikin matsala.

Wani fitaccen lauya a Najeriya, Deji Ajare ya bukaci Majalisar jihar Kogi ta tsige Gwamna Ododo kan hawan ƙawara ga dokokin kasa.

Kara karanta wannan

"Ɗaurin shekaru 5": EFCC ta ja kunnen gwamnan APC da masu kawo cikas kan Yahaya Bello

Gwamna Kogi ya shiga matsala kan ceton Yahaya Bello
Lauya ya bukaci tsige gwamnan Kogi kan sulalewa da Yahaya Bello. Hoto: Usman Ododo, Yahaya Bello.
Asali: Facebook

Wace bukata lauyan ya gabatar kan Ododo?

Ajare ya ce abin da gwamnan ya aikata na tserewa da Yahaya Bello ya saba dokar kasa wanda ya cancanci hukunci, kamar yadda ya wallafa a shafin Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bukaci kakakin Majalisar, Umar Yusuf da ya fara shirin tsige gwamnan da gaggawa saboda neman maslaha kan abin da ya aikata.

Wannan na kunshe ne a cikin wata takarda da lauyan ya tura zuwa hannun magatakardan Majalisar a yau Juma'a 19 ga watan Afrilu.

Lauya ya bayyana 'laifuffukan' Ododo a mulki

Ya ce sulalewa da gwamnan ya yi da mai gidansa ya aikata babban laifi na kawo cikas ga shari'a da kuma boye mai laifi.

Har ila yau, lauyan ya bukaci Majalisa da ta haɗa kai da hukumar EFCC domin tabbatar da dukkan masu laifin sun gurfana domin amsa tambayoyi.

Kara karanta wannan

EFCC: An yi ta harbe-harbe yayin da Gwamnan Kogi ya sulale da Yahaya Bello

Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Ododo ya tsere da mai gidansa, Yahaya Bello a idon jami'an hukumar EFCC.

EFCC na neman Bello ruwa a jallo

A wani labarin, hukumar EFCC ta sanar da cewa tana neman Yahaya Bello ruwa a jallo bayan zargin almundahana da ke kansa.

Hukumar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa a jiya Alhamis 18 ga watan Afrilu inda ta ke neman tsohon gwamnan ko ta halin yaya.

Hakan ya biyo bayan yunkurin cafke tsohon gwamnan da hukumar ta yi amma ba ta yi nasara ba a ranar Laraba 17 ga watan Afrilu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.