Jiga-Jigan PDP Sun Cimma Matsaya Kan Kujerar Shugaban Jam'iyyar na Kasa
- Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta tsawaita wa’adin shugaban riƙo na jam’iyyar na ƙasa, Ambasada Umar Damagum
- Jam'iyyar ta ƙara wa'adin Damagum ne a matsayin shugaban riƙo domin tabbatar da sulhu da haɗin kai a jam'iyyar hamayyar
- Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce ƙarin wa’adin ya dogara ne da shawarar da za a yanke a taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC)
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - An ƙara wa'adin muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa, Ambasada Umar Damagum.
Sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar PDP na ƙasa, Debo Ologunagba, ya ce jam’iyyar ta ɗauki matakin ne domin tabbatar da sulhu da haɗin kai a cikinta.
TABLE OF CONTENTS
Ologunagba ya bayyana haka ne bayan kammala taron jiga-jigan jam’iyyar PDP a masaukin gwamnan jihar Bauchi da ke Asokoro, Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Karin wa'adin Umar Damagum a PDP?
Kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito, ƙarin wa’adin ya dogara ne kan shawarar da za a yanke a taron kwamitin zartaswa na ƙasa wanda za a gudanar a ranar Alhamis, 18 ga watan Afirilun 2024.
"Umar Damagum zai ci gaba da zama muƙaddashin shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa har zuwa taron NEC na gaba. Jam'iyyar ta lura cewa yana da muhimmanci a sake tattaunawa sosai kan wannan batun."
- Debo Ologunagba
The Punch ta ce a lokuta da dama idan ƙusoshin PDP na ƙasa suka cimma matsaya, taron NEC yana amincewa da ita, amma idan an samu saɓani sauran mambobin NEC su kan kaɗa ƙuri'ar amincewa ko ƙin amincewa da batun.
Atiku ya haɗu da Wike a taron PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya haɗu da Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP a zaɓen 2024.
Manyan ƴan siyasan biyu sun haɗu ne a wajen taron manyan ƙusoshin jam'iyyar PDP na ƙasa da aka gudanar a birnin tarayya Abuja.
Asali: Legit.ng