Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Sauya Sheƙa Daga Jam'iyyar PDP Zuwa APC

Tsohon Mataimakin Shugaban Majalisa Ya Sauya Sheƙa Daga Jam'iyyar PDP Zuwa APC

  • Tsohon mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Ondo ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyyar APC mai mulki
  • Ogundeji Iroju ya ɗauki wannan mataki ne yayin da Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya je ƙaramar hukumar Odigbo domin neman kuri'un mambobin APC
  • Gwamnan ya bayyana cewa zai ƙarisa aikin tashar ruwa da tsohon gwamna, Marigayi Akeredolu ya fara domin bunƙasa tattalin arziƙi

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ondo - Tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Ondo, Ogundeji Iroju, ya fice daga Peoples Democratic Party (PDP) zuwa jam'iyyar APC mai mulki.

Iroju ya koma APC ne lokacin da Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya ziyarci karamar hukumar Odigbo a wani ɓangare na ci gaban da yawon neman ƙuri'un mambobin jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Babban jigon APC ya aike da saƙo ga ƴan majalisar tarayya 60 da ke shirin sauya sheƙa

Gwamnan Ondo, Lucky Aiyedatiwa.
Gwamnan Ondo ya ci gaba da yawon neman kuri'un mambobin jam'iyyar APC Hoto: Hon. Lucky Aiyedatiwa
Asali: Facebook

Gwamna Aiyedatiwa ya kuma ziyarci garuruwa da dama da suka haɗa da Igbokoda, Ilaje da Okitipupa domin roƙon ƴaƴan APC su zaɓe shi a zaɓen fitar da gwani, cewar The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan APC ya ɗauki alƙawurra

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da aikin tashar ruwan Ondo da ƙara dagewa kan aikin gwamnatin tarayya na maido da wutar lantarki a yankin Sanatan Ondo ta kudu.

Aiyedatiwa ya yi nuni da cewa ya gaji aikin tashar jiragen ruwa daga marigayi Oluwarotimi Akeredolu, wanda dole ne ya ƙarisa domin ci gaban tattalin arzikin jihar.

“Game da batun wutar lantarki, daya daga cikin ‘ya’yanmu da ke aiki da NDDC ya ci gaba da aikin kuma an kammala kashi 98% kawo yanzu.
"Kamfanin rarraba wutar lantarki BEDC yana fama da kalubalen mita kuma tunda mutane da yawa suna bin su bashi, ba za su iya siyan mitoci ga daidaikun mutane ba.

Kara karanta wannan

Kano: Jigon APC ya faɗi matakin da ya kamata Tinubu ya ɗauka a rikicin Kwankwaso da Ganduje

“Gwamnatinmu za ta taimaka wajen siyan mitoci kamar yadda na umarci wadanda ke da alhakin su yi lissafin kudin. Da zaran an kammala za a dawo da wutar lantarki.”

- Lucky Aiyedatiwa.

Gwamnan ya ce idan har mutane na son wannan ya ci gaba, ya zama dole su haɗa kai su fito ranar Asabar da katunan su na jam'iyya kana su zabe shi.

Jigon APC ya roƙi ƴan majalisar PDP

A wani ɓangaren kun ji cewa Jigon APC ya buƙaci ƴan majalisar tarayya 60 da suka yi barazanar ficewa daga jam'iyyar PDP da su sauya tunani.

Ƴan majalisun sun gindaya sharaɗin cewa matukar Umar Damagum ya ci gaba da zama a kujerar shugaban PDP, za su tattara su koma wasu jam'iyyun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262