Malam El-Rufa'i Ya Bayyana Sunan Gwamnan da Ya Fi Sauran Gwamnoni Aiki a Najeriya

Malam El-Rufa'i Ya Bayyana Sunan Gwamnan da Ya Fi Sauran Gwamnoni Aiki a Najeriya

  • Tsohon gwamnan Kaduna El-Rufa'i ya ce Gwamna Babagana Umaru Zulum ya fi kowane gwamna kokari a Najeriya a halin yanzu
  • Malam Nasir El-Rufa'i ya ce duk da halin ƙuncin da Boko Haram ta jefa Borno na tsawon lokaci amma duk lokacin da shigo sai ya ji farin ciki
  • A cewarsa, duba da yadda abubuwa suka fara gyaruwa a Maiduguri, babu shakka Borno ta samu jagoranci nagari a karkashin Zulum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Borno - Malam Nasir El-Rufa'i ya bayyana Gwamna Babagana Zulum na jihar Borno a matsayin gwamna mafi nagarta a Najeriya a halin yanzu.

Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar Kaduna ya yi wannan jawabi ne a wani taron karawa juna sani na inganta karfin aiki ga manyan jami’an gwamnatin Borno, ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Kano: Muhuyi Magaji ya yi magana kan fara binciken Gwamna Abba, ya taɓo Ganduje

Babagana Umaru Zulum.
Malam El-Rufai ya yabawa da sabon shugabancin Zulum a jihar Borno Hoto: Prof. Babagana Umara Zulum
Asali: Facebook

Taron ya gudana ne a Maiduguri, babban birnin jihar Borno kuma El-Rufai ne babban baƙo mai jawabi, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A jawabinsa, tsohon gwamnan Kaduna ya bayyana gazawar shugabanci a matsayin babbar matsalar Najeriya.

El-Rufai ya yabawa Zulum

Malam Nasiru ya kuma yabawa salon mulkin Gwamna Zulum wajen sake gina jihar Borno da kuma farfaɗo da tattalin arziƙi, rahoton Within Nigeria.

"Ina ganin Farfesa Zulum shi ne gwamnan da ya fi kowane gwamna aiki a kasar nan. Zan yi magana a kan hakan daga baya,” in ji shi.

El-Rufa'i ya ƙara da cewa abin farin ciki ne ganin yadda jihar ta yi kyau kuma an samu sauƙi duk da tsawon shekarun da aka kwashe ana fama da rikicin Boko Haram.

Yadda Zulum ke gyara Borno

Kara karanta wannan

Malam El-Rufai ya faɗi Ministoci da Hadiman da ya kamata Tinubu ya kora daga aiki

"Ina jin daɗin zuwa Borno a kowane lokaci, duk da ban cika kawo ziyara ba amma duk lokacin da na zo ina farin ciki da abubuwan da nake gani, musamman yadda Maiduguri ta ginu, ga tsafta da tsari da zirga-zirga.
"Wutar lantarki ta dawo kuma mutane na samun damarmaki na tattalin arziki. Tashin hankalin Boko Haram, kashe-kashe da katse wutar lantarki duk ya wuce, hakan ya nuna nagartar shugabancin da kuke da shi a Borno.

- in ji El-Rufa'i.

Tsohon gwamnan ya kuma tabbatar da cewa har yanzun gwamnatin tarayya na biyan tallafin man fetur, kuma kuɗin da ake biya yanzu ya zarce na baya.

Saƙon El-Rufai ga Tinubu

A wani rahoton na daban tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Tinubu kada ya ji kunyar korar duk ministan da ya kasa komai

El-Rufai ya ce dukkan ministoci ko hadiman da shugaban ƙasa ya naɗa, idan suka gaza kai matakin da ake tsammani, ya sallame su daga aiki

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262