Jam'iyyar APC Ta Hukunta Wadanda Suka Dakatar da Ganduje, Ta Zayyano Laifukansu
- Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC a jihar Kano ya ladabtar da shugabannin jam'iyyar da suka dakatar da Abdullahi Umar Ganduje
- Shugabannin APC dai na mazaɓar Ganduje sun dakatar da shugaban jam'iyyar na ƙasa bisa tuhume-tuhumen cin hanci da rashawa
- Shugaban APC na jihar ya ce waɗanda suka dakatar da Ganduje masu cin dunduniyar jam'iyyar ne kuma za a bincike su
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Kwamitin gudanarwa na jam'iyyar APC a jihar Kano, ya hukunta wasu shugabannin jam'iyyar na matakin mazaɓa.
Shugabannin dai su ne suka dakatar da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje.
Shugabannin jam'iyyar na mazaɓar Ganduje a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa sun sanar da dakatar da shugaban jam'iyyar APC na ƙasa a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai, cikin hanzari shugabannin jam'iyyar a matakin ƙaramar hukuma sun yi fatali da dakatarwar tare da korar waɗanda ke da hannu a cikinta, cewar rahoton jaridar The Nation.
Meyasa APC ta kori shugabannin?
Shugaban jam'iyyar APC na ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, Inuwa Dawanau, ya bayyana cewa waɗanda ke da hannu a dakatar da Ganduje an kama su da laifin cin dunduniyar jam'iyyar.
Ya ƙara da cewa suna da dukkanin bayanai kan lokutan da suka riƙa ganawa da ƴan adawa, rahoton jaridar Leadership ya tabbatar.
Da yake amincewa da dakatar da shugabannin, kwamitin gudanarwar ya ce an dakatar da su na tsawon wata shida sannan an kafa kwamitin bincike na musamman kan zarge-zargen da ake yi musu.
Shugaban jam'iyyar APC na jihar Kano, Abdullahi Abbas, ya ce tuni aka amince da matakin da shugabannin jam'iyyar na ƙaramar hukumar suka ɗauka.
Game da batun binciken Ganduje
A wani labarin kuma, kun ji cewa wata ƙungiya a ƙarƙashin ƙungiyar Kano Concerned Forum (KCF) ta yi Allah-wadai da shirin gwamnatin jihar Kano na binciken gwamnatin tsohon Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Ƙungiyar ta bayyana cewa dawo da batun binciken gwamnatin Ganduje, alamu ne na cewa gwamnatin yanzu ta yarda da cewa ta kasa taɓuka komai.
Asali: Legit.ng