Ana Daf Da Zabe, Tsohon Sanata da Ɗan Majalisa Sun Watsar da PDP, Sun Koma APC
- Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta yi babban kamu yayin da jiga-jigan jam'iyyar PDP suka sauya sheka
- Jiga-jigan jam'iyyar sun watsar da PDP ne a yau Asabar 13 ga watan Afrilu inda APC ta tarbesu a birnin Benin City
- Wanna na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaben gwamnan jihar a ranar 21 ga watan Satumba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Edo - Yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen gudanar da zabe a jihar Edo, PDP ta samu babban naƙasu.
Jam'iyyar ta rasa wasu jiga-jigai da suka hada da tsohon Sanata da kuma mamban Majalisar Wakilai bayan sun koma jam'iyyar APC.
Wasu jiga-jigan PDP ne suka koma APC?
Sanata Matthew Uhroghide wanda ya wakilci Edo ta Kudu har sau biyu a Majalisar Tarayya da kuma tsohon dan Majalisar Wakilai, Patrick Giwa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sauran sun hada da magatakardan Majalisar Tarayya da tsoffin ciyamomi da mataimakansu a mulkin Gwamna Godwin Obaseki, cewar Channels TV.
Sabbin tuban sun samu tarba daga jiga-jigan jam'iyyar APC a yau Asabar 13 da watan Afrilu a birnin Benin City da ke jihar, cewar AIT News.
Tsohon gwamnan Abia ya ƙaryata komawa APC
Har ila yau, Tsohon gwamnan jihar Abia, Dakta Okezie Ikpeazu ya yi martani kan jita-jitar cewa ya na shirin komawa APC.
Ikpeazu ya ƙaryata maganar inda ya ce ko kusa babu wani shirin da ya ke da shi na barin jam'iyyar PDP tare da komawa APC.
Hakan ta biyo bayan komawa jami'yyar APC mai mulki da wasu jiga-jigan PDP suka yi a jihar ciki har da tsoffin mukarrabansa.
An tsige mataimakin gwamnan Edo
A baya, mun ruwaito muku cewa Majalisar jihar Edo ta tsige mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu.
An tsige Shaibu ne bayan wasu zarge-zarge da suka hada da bankada asirin gwamnatin jihar da sauran laifuffuka.
Wannan na zuwa ne yayin da alaka ta yi tsami tsakanin Gwamna Godwin Obaseki da tsohon mataimakinsa, Philip Shaibu.
Asali: Legit.ng