Cikakken Sakamako: Jam'iyyar PDP Ta Lashe Zaben Ciyamomi 8 da Kansiloli 105 a Jiha 1
- Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta jihar Bayelsa (BYSIEC) ta sanar da sakamakon zaben kananan hukumomin da aka yi ranar Asabar
- Jam'iyyar PDP mai mulkin jihar ta lashe dukkan kujerun ciyamomi 8 da kansiloli 105 a faɗin jihar Bayelsa
- Tun farko dai jam'iyyar APC ta bayyana cewa ba za ta shiga zaɓen ba kuma ba ta tsayar da ƴan takara ko ɗaya ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bayelsa - Jam’iyyar PDP mai mulki a jihar Bayelsa ta lashe zaben dukkan kananan hukumomin da hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar ta gudanar a ranar Asabar.
Jam’iyyar PDP ta lashe zaben ciyamomi a dukkanin kananan hukumomi takwas na jihar Bayelsa da kuma dukkan kujerun kansiloli a gundumomi 105.
Hakan na kunshe ne a sakamakon zaben da hukumar zaɓen ta sanar ranar Lahadi, 7 ga watan Afrilu, 2024 a Yenagoa, babban birnin jihar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda jaridar Punch ta rahoto, babbar jam'iyyar adawa a jihar watau APC ta ƙauracewa zaɓen gaba ɗaya domin ba ta tsayar da ƴan takara ba.
Sakamakon kowace ƙaramar hukumar Bayelsa
A karamar hukumar Yenagoa, jami'ar BYSIEC, Wisdom Soreh, ta bayyana Bulodisiye Ndiwari a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 56,103.
Baturen zaɓen a karamar hukumar Sagbama, Farfesa Abiodun Adelegan, ya bayyana Alice Tangi a matsayin wanda ta lashe zaben. Ta samu kuri'u 51,543.
A karamar hukumar Ogbia, jami’in zabe, Tams Deiduomo, ya bayyana Golden Jeremiah, wanda ya samu kuri’u 42,462, a matsayin wanda ya lashe zaben.
Baturen zaɓen karamar hukumar Kudancin Ijaw, Ebi Stanley-Udisi, ya bayyana Target Segibo a matsayin wanda ya lashe zaben, inda ya samu kuri’u 36,326.
A karamar hukumar Nembe, tsohon kwamishinan noma, David Alagoa, ya samu kuri’u 11,829 wanda ya ba shi damar lashe zaben in ji baturen zaɓen, Farfesa Festus Akpotohwo.
A karamar hukumar Kolokuma/Opokuma, jami’in zabe Farfesa Apuega Arikawei, ya bayyana Lelei Tariye a matsayin wanda ya samu nasara a zaben da kuri’u 27,823.
Haka kuma, jami’in zabe na karamar hukumar Ekeremor, Farfesa Joseph Omoro, ya bayyana Onniye Isaac a matsayin wanda ya lashe zaben da kuri’u 35,177, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.
Jigawa ta kafa kwamitin bincike
A wani rahoton kuma Gwamnatin Jigawa a karkashin Gwamna Umar Namadi ta kafa kwamitin bincike kan abin da ya faru a shirin ciyarwa na Ramadan
Kwamishinan yaɗa labarai, Sagir Musa, ya ce za a gudanar da bincike ne kan zargin karkatar da kuɗaɗen shirin a karamar hukumar Babura
Asali: Legit.ng