Yan Majalisar Tarayya 60 Sun Yi Barazanar Ficewa Daga Jam'iyyar PDP, Sun Faɗi Buƙata 1

Yan Majalisar Tarayya 60 Sun Yi Barazanar Ficewa Daga Jam'iyyar PDP, Sun Faɗi Buƙata 1

  • Jam'iyyar PDP ta sake shiga sabuwar matsala yayin da ƴan majalisar wakilan tarayya 60 suka yi barazanar ficewa daga cikin jam'iyyar
  • Ƴan majalisun sun yi barazanar barin PDP ne matuƙar ba a sauya muƙaddashin shugaban jam'iyyar, Umar Damagum ba
  • Sun buƙaci Damagum ya yi murabus kuma a maye gurbinsa da ɗan shiyyar Arewa maso Tsakiya kamar yadda tsarin mulkin PDP ya tanada

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Aƙalla mambobin majalisar wakilan tarayya 60 na jam'iyyar PDP sun yi barazanar ficewa daga babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa.

Ƴan majalisun sun yi barazanar fita daga PDP matuƙar muƙaddashin shugaban jam'iyyar na ƙasa, Umar Damagum, bai yi murabus daga muƙaminsa ba.

Kara karanta wannan

InnalilLahi: Ƴan bindiga sun halaka jami'an tsaro 30 ana shirin ƙaramar sallah a Arewa

Taron PDP.
Mambobin majalisar wakialai na PDP sun ɗauki zafi Hoto: OfficialPDPNig
Asali: Twitter

'Yan siyasar sun buƙaci Damagum ya yi murabus kuma a maye gurbinsa da wani ɗan yankin Arewa ta Tsakiya nan take kamar yadda kundin dokokin jam'iyyar PDP ya tanada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ƴan majalisar tarayyar sun kuma gindaya wasu sharuɗɗa bayan wannan, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Meyasa suka yi wannan barazana?

'Yan majalisar sun zargi Damagum da mika tsarin shugabancin jam’iyyar PDP ga jam’iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Honorabul Ugochinyere Ikenga ne ya bayyana haka a madadin sauran ƴan majalisa 60 yayin hira da manema labarai ranar Litinin a Abuja.

Ya ce suna zargin muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Damagum da cin amanar jam'iyyar kuma ga dukkan alamu ya cefanar da su.

Ikenga ya yi nuni da cewa da a ce shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bai tsaya tsayin daka a tsagin adawa na tsawon shekaru ba, da bai samu nasarar zama shugaban kasa ba.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kai farmaki kan dan majalisa har cikin gida a jihar Arewa

Damagum na shirin rusa PDP?

A cewarsa, ya zama wajibi Damagun ya kama gabansa tun kafin ya kammala ida aniyarsa ta rusa babbar jam'iyyar adawa.

‘Yan majalisar sun yi barazanar cewa idan har aka gaza cika waɗannan buƙatu, to za su fice daga PDP su koma wasu jam’iyyun siyasa, rahoton Channels tv.

Matashi ya zama mataimakin gwamna

A wani rahoton kuma Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo ya ɗauki sabon mataimakin gwamna jim kaɗan bayan majalisar dokoki ta tsige Kwamred Philip Shaibu.

Bayanai sun nuna cewa shirye-shirye sun yi nisa wajen rantsar da Marvellous Omobayo Godwin a gidan gwamnati da ke Benin ranar Litinin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262