Majalisar Dattawa Na Shirin Ɗage Dakatarwan da Ta Yi Wa Sanata Abdul Ningi. Ya Faɗi Dalili

Majalisar Dattawa Na Shirin Ɗage Dakatarwan da Ta Yi Wa Sanata Abdul Ningi. Ya Faɗi Dalili

  • Sanata Godswill Akpabio ya ce nan ba da daɗewa ba majalisar dattawa za ta ɗage dakatarwar da ta yi wa Sanata Abdul Ningi mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya
  • Shugaban majalisar ya bayyana haka ne yayin da yake hira da ƴan jarida jim kaɗan bayan ya dawo Najeriya daga wurin taro a ƙasar Switzerland
  • Wannan kalamai na zuwa ne sa'o'i 24 bayan Ningi ya yi barazanar ɗaukar matakin shari'a idan ba a janye dakatarwar ba cikin mako ɗaya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya ce nan ba da dadewa ba majalisar za ta ɗage dakatarwar da ta yi wa Sanata Abdul Ningi (PDP, Bauchi ta Tsakiya).

Kara karanta wannan

Abin da Bola Tinubu ya faɗawa manyan Malamai da Sarakuna a wurin buɗa baki a Aso Villa

Hakan na zuwa ne sa’o’i 24 bayan sanatan ya rubuta wasiƙa ga Akpabio, inda ya yi barazanar daukar matakin shari’a idan ba a dage dakatarwar da aka yi masa ba cikin kwanaki 7.

Akpabio da Abdul Ningi.
Nan ba da daɗewa ba za a ɗage dakatarwar Sanata Ningi Hoto: Senator Godswill Akpabio, Abdul Ningi
Asali: Facebook

Meyasa majalisa ta dakatar da Ningi?

An dakatar da Ningi ne biyo bayan zargin da ya yi cewa an yi cushen N3.7m a kasafin kudin shekarar 2024, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayan zazzafar muhawara da Sanatoci suka yi a zauren majalisa kan lamarin, an dakatar da Ningi na tsawon watanni uku tare da neman ya rubuta wasikar neman gafara.

Ningi ya yi barazanar shiga kotu

Sai dai a wata wasika da lauyansa, Femi Falana (SAN) ya rubuta, Ningi ya zargi Akpabio da zama alkali, wanda ake ƙara, da wanda ke a ƙara a kes ɗin, wanda ya saba kundin tsarin mulki.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Gwamnan PDP ya naɗa tsohon shugaban tsageru a matsayin Sarki mai martaba

Sanatan ya zargi Akpabio da sa a gurfanar da shi a gaban majalisar dattawa ranar 14 ga Maris, 2024 wanda ya saba wa tanade-tanaden dokokin majalisun dokoki 2018, rahoton The Cable.

Majalisa za ta sake duba lamarin

Amma da yake amsa tambayoyin ƴan jarida ranar Juma’a bayan ya dawo daga taron kungiyar ‘yan majalisa a birnin Geneva na kasar Switzerland, Akpabio ya ce nan ba da dadewa ba majalisar dattawa za ta sake nazari.

"Majalisa ta ɗauki matakin, ni ban ga takardar ba amma Sanata Ningi ɗaya daga cikinmu ne, menene dakatarwa? Ina da yaƙinin nan da ƴan kwanaki zai dawo cikinmu.
"Saboda haka babu wata matsala, zamu warware lamarin cikin ruwan sanyi, mun ƴan gida ɗaya ne."

- Godswill Akpabio.

Majalisar dattawa dai na shan matsin lamba kan ta sake nazari kan matakin da ta ɗauka wanda ake ganin kwata-kwata bai dace ba.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Malam Nasiru El-Rufa'i ya gana da fitaccen sanatan PDP, hotuna sun bayyana

El-Rufai ya gana da Sanata Ningi

A wani rahoton na daban Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai, ya kai ziyara gidan Sanata Abdul Ningi, wanda majalisar dattawa ta dakatar kwanan nan.

Majalisa ta dakatar da Sanata Ningi, mamban jam'iyyar PDP mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya saboda zargin cushe a kasafin kuɗin 2024.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262