Zaben 2027: Peter Obi Zai Fice Daga Labour Party? Gaskiya Ta Bayyana
- Kakakin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa jam'iyyar Labour Party (LP), Yunusa Tanko ya musanta raɗe-raɗin ficewar Peter Obi daga jam'iyyar
- Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da rikicin cikin gida kan shugabancin jam’iyyar ya haifar da shakku kan makomar Obi a jam’iyyar
- Tanko ya fayyace cewa Obi zai ci gaba da zama a jam’iyyar LP, tare da bada cikakken goyon baya wajen inganta muradun jam’iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Yunusa Tanko, kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), ya tabbatar da cewa Peter Obi, ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar a zaɓen 2023, ba shi da niyyar ficewa daga jam'iyyar.
Tanko, a wata tattaunawa da jaridar TheCable, ya bayyana cewa Obi yana nan daram a jam’iyyar LP, kuma baya tattaunawa da kowa domin yiwuwar kafa sabuwar jam’iyyar siyasa.
Duk da dambarwar da jam'iyyar ta samu kanta a baya, ciki har da kiran da magoya bayan Obi suka riƙa yi na ya fice ya kafa sabuwar jam'iyya, Tanko ya bada tabbacin cewa ba zai bar jam'iyyar ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Peter Obi na nan daram a LP' - Tanko
Tanko ya fayyace cewa, duk da halin da ake ciki, Obi ya ci gaba da kasancewa cikakken ɗan jam’iyyar LP tare da tsayawa tsayin daka wajen ci gaban jam'iyyar.
A kalamansa:
"Aa ko kaɗan. A halin yanzu dai ba ya tunanin barin jam'iyyar Labour Party.
"Mai girma, Mista Peter Obi, na ƙoƙarin gina wani dandali da zai ɗauki kowa da kowa. Ko shakka babu ya ƙara ɗaga ƙimar jam'iyyar.
"A yanzu dai, bai ce komai ba dangane da barin jam'iyyar ba. Idan har akwai wannan shirin, da tuni mun san da shi.
"Yana kare jam'iyyar LP da duk iyakar iyawarsa. Abin da muka sani shi ne idan akwai matsaloli a cikin jam'iyyar, abin da kawai muke buƙata shi ne mu yi gyare-gyaren da suka dace ba tare da ɓata lokaci."
Batun buɗa bakin Peter Obi
A wani labarin kuma, kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party (LP), Yunusa Tanko, ya kare matakin Peter Obi na yin buɗa baki tare da musulmai a watan azumin Ramadan.
Yunusa ya ce matakin na Obi ba siyasa ba ce domin dama tun asali ya saba yin cuɗanya da talakawa.
Asali: Legit.ng