Kano: Jigon NNPP Ya Magantu Kan Koma Bayan Farin Jinin Jam’iyya, Ya Fadi Mafita
- Wani jigon jam’iyyar NNPP a jihar Legas, Razaq Adebirigbe ya tabbatar da cewa jam’iyyarsu na fuskantar kalubale
- Jigon jam’iyyar ya ce yana da tabbacin za ta tsallake kalubalen da ta ke fuskanta musamman a jihar Kano
- Razaq ya bayyana haka ga Legit inda ya ce jam’iyyar ba za ta kaucewa tsarinta na inganta rayuwar al’ummar da ta ke jagoranta ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, yana da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano – Jigon jam’iyyar NNPP a Najeriya, Razaq Adebigbe ya ce jam’iyyar a jihar Kano ta na nan da karfinta.
Razaq ya bayyana haka ne yayin da ake jita-jitar cewa jam’iyyar ta fara samun rauni a jihar saboda wasu matsaloli.
Menene jigon NNPP ke cewa kan jam'iyyar?
Jagoran ya ce karfin jam’iyyar ya na nan kuma ba za ta sauka kan tsarinta na ingata rayuwar al’ummar jihar Kano ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa wannan ba bakon abu ba ne jam’iyya ta fuskanci wasu kalubale musamman a wurin jam’ar da ta ke mulka.
Jigon Jam’iyyar ya fadawa Legit cewa:
“Yayin da muke fuskantar kalubale, ya kamata a duba yadda juyin siyasa ke tafiya da kuma juyawar lamura musamman daga mutane.”
“A matsayin jam’iyya, za mu ci gaba da dogewa kan bin tsari da kuma inganta al’ummar kasa baki daya.”
Kwarin gwiwarsa kan jam'iyyar NNPP
“Duk da matsalolin da aka samu, mun himmatu wurin tabbatar da cewa ba mu kauce kan tsarin jam’iyyar ba kamar yadda muka yi nasara a shari’ar jihar Kano haka za mu sake wuce wannan.”
- Razaq Aderibigbe
Jigon NNPP ya ce ana iya samun irin wadannan matsaloli saboda wasu dalilai da suka shafi siyasa da kuma tattalin arziki.
Gwamnatin NNPP za ta kashe N6bn a Kano
Kun ji cewa Gwamnatin NNPP a karkashin Abba Kabir na jihar Kano ta ware makudan kudi har N6bn domin ciyar da mutane a Ramadan.
Wannan mataki na gwamnan na zuwa ne yayin da ake cikin wani yanayi na tsadar kayan abinci gami da fara azumin watan Ramadan mai albarka.
Asali: Legit.ng