Bello El-Rufai Ya Bayyana Adadin Miliyoyin da Mahaifinsa Ya Ba Shi da Ya Fito Takara
- Muhammad Bello El-Rufai ne ya yi wa jam’iyyar APC takarar ‘dan majalisa mai wakiltar Kaduna ta Arewa a zaben 2023
- Duk da yana sabon ‘dan siyasa, babban yaron gwamnan ya samu karbuwa musamman ganin yadda yake bada taimako
- A lokacin mahaifinsa ne gwamna a jihar Kaduna, N5m ya ba shi a matsayin gudumuwarsa wajen yakin neman takara a APC
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Abuja - Muhammad Bello El-Rufai ya yi wata doguwar hira a watan nan na Maris, inda ya tattauna a game da batutuwa da yawa.
Seun Okinbaloye ya zanta da Hon. Muhammad Bello El-Rufai a shirinsa Mic On, inda ‘dan majalisar ya bada labarin yakin zabensa.
Gudumuwar El-Rufai ga 'dansa a zaben 2023
‘Dan majalisar mai wakitar Kaduna ta Arewa ya ce a lokacin da yake neman takara a 2023, Naira miliyan biyar mahaifinsa ya ba shi.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A lokacin da Bello El-Rufai ya tsaya takarar kujerar majalisar wakilan tarayya, mahaifinsa Nasir El-Rufai shi ne gwamnn Kaduna.
Takarar Bello El-Rufai zuwa majalisar tarayya
A cewar ‘dan majalisar, a lokacin Mai girma Uba Sani yana Sanata, sai ya kawowa gwamnan shawarar takarar Bello El-Rufai a 2023.
Kamar yadda ya shaida a shirin na Podcast, Malam Nasir El-Rufai bai yi maraba da shawarar nan ba saboda wasu dalilai da ya kawo.
El-Rufai ya so takarar yaron da ya haifa?
Daga ciki shi ne tsohon gwamnan na Kaduna bai son ganin ana neman maida mulkin tamkar wani gadon gidan Nasir El-Rufai.
‘Dan majalisar ya kuma ce daga baya mahaifinsa ya bayyana masa yana da saurin fushi, saboda haka bai dace da wakilcin jama'a ba.
An bijiro batun takarar ne a birnin Dubai, Malam Bello El-Rufai ya so a ce gudumuwar yakin zaben da gwamna ya ba da ya wuce N5m.
Bello El-Rufai ya zama wakili a majalisa
Yayin kamfe, Bello El-Rufai ya shiga kowace mazaba da ke Kaduna ta Arewa, kuma a karshe ya tashi da kuri’u fiye da 51, 000 a APC.
Kamar yadda babban yaron gwamnan ya fada, sun yi tsari da kyau, tun kafin ya lashe zabe yake bada tallafi, a karshe ya doke PDP.
‘Dan siyasar ya jero inda suka sha bam-bam da mahaifin nasa, daga ciki shi ne ko kadan Malam El-Rufai bai sha’awar kujerar majalisa.
An hana El-Rufai zama ministan tarayya
A baya ana da labari dan majalisar tarayya, Bello El-Rufai ya fadi yadda ya ji bayan kin amincewa da mahaifinsa ya zama minista.
Nasir El-Rufai ya samu matsala a majalisa yayin tantance wadanda za su zama ministoci, inda aka fake da wani rahoton tsaro.
Asali: Legit.ng