Kakakin Kwamitin Kamfen Atiku Ya Faɗi Muhimman Abubuwa 2 da Najeriya Ke Bukata Kafin Zaɓen 2027

Kakakin Kwamitin Kamfen Atiku Ya Faɗi Muhimman Abubuwa 2 da Najeriya Ke Bukata Kafin Zaɓen 2027

  • Daniel Bwala ya bayyana cewa ya zama dole a samu tsaro da kwanciyar hankali a Najeriya gabanin babban zaben 2027
  • Tsohon kakakin kwamitin kamfen Atiku/Okowa a inuwar PDP ya yabawa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa sauye-sauyen da ya fara
  • Ya ce duk da yana goyon bayan gwamnatin Tinubu a yanzu, bai taɓa jin nadamar komawa PDP da goyon bayan Atiku Abubakar ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Tsohon kakakin kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Atiku Abubakar wanda aka rushe, Daniel Bwala, ya fara taɓo batun babban zaɓen 2027.

Mista Bwala ya bayyana cewa ya zama wajibi Najeriya ta samu zaman lafiya da kwanciyar hankali gabanin babban zaɓe na gaba.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya jero mutanen da suka koma yaƙarsa saboda matakan da ya ɗauka a Najeriya

Shugaba Tinubu da Daniel Bwala.
Dole ne Najeriya ta kasance cikin kwanciyar hankali kafin zaben 2027 – Daniel Bwala Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Daniel Bwala
Asali: Twitter

Babban jigon PDP ya yi wannan furucin ne yayin hira da Arise Tv ranar Jumu'a, 15 ga watan Maris, 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon mai magana da yawun kamfen Atiku ya kuma yabawa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, bisa ƙoƙarin da gwamnatinsa ke yi na kawo sauyi mai amfani.

Bwala ya jaddada goyon bayansa ga Tinubu

Bwala, ya ce bai taɓa yin nadamar komawa jam’iyyar Peoples Democratic Party, (PDP) ba, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

“Ban yi dana sani ko nadamar shiga PDP ko goyon bayan Atiku ba, ina tafiyar da harkokina yadda ya kwanta mun a rai kuma a karshe, idan har hakan bai yi nasara ba, ina yarda da kaddara ta."
“Ina ganin cewa wannan shugaban ƙasa da nake goyon baya a APC (Bola Ahmed Tinubu) yana kokarin kawo sauyi a kura-kuran da gwamnatin da ta gabata ta tafka."

Kara karanta wannan

Shugabannin APC sun faɗawa Tinubu mataki 1 da ya kamata ya ɗauka kan wasu hafsoshin tsaro a Najeriya

"Lokacin da ya ce yana son duk ‘yan adawa su taho a haɗa kai a gina kasa, sai na ga lokaci ya yi da za a kalli gina kasa maimakon siyasa. Ba zamu iya yin siyasa ba sai har idan Najeriya ta zauna lafiya."

- Daniel Bwala.

Tinubu ya jero masu yaƙar gwamnatinsa

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya ce masu amfana da tallafin man fetur a ƴan fasa kwauri ba su haƙura ba, sun koma suna yaƙar gwamnati.

Yayin ganawa da shugabannin APC na jihohi, Tinubu ya jaddada cewa gwamnatinsa na aiki ba dare ba rana domin inganta rayuwar jama'a.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262