Tinubu Ya Canza Tunani, Ya Janye Sunan Matar da Ya Naɗa a Babban Banki CBN, An Gano Dalili
- Ruby Onwudiwe, matar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya naɗa a matsayin darakta a CBN ta gamu da cikas saboda alaƙarta da LP
- Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun faɗa wa shugaban kasa cewa bai kamata ya naɗa ta a matsayin mamban majalisar gudanarwa ta CBN ba
- A martanin da ya yi game da kiraye-kiragen ƙusoshin APC, Tinubu ya buƙaci majalisar dattawa ta jingine batun naɗin Onwudiwe
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya janye naɗin Ruby Onwudiwe a matsayin mambar majalisar gudanarwa ta babban bankin Najeriya (CBN).
Rahotanni sun nuna cewa shugaban ƙasa ya ɗauƙi wannan matakin ne biyo bayan matsin lambar da yake fuskanta daga mambobin jam'iyyar APC mai mulki.
Meyasa Tinubu ya janye naɗin Onwudiwe?
An tattaro cewa wasu jiga-jigan APC sun matsawa Tinubu lamba cewa bai kamata ya naɗa matar a CBN ba duba da alaƙarta da siyasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kamar yadda The Cable ta ruwaito, Onwudiwe ta wallafa wani sako a shafinta na X lokacin zaɓen 2023, inda ta ce, "Labour Party ta samu gagarumar nasara a akwatin zaɓe na da ke Lekki."
Wannan dalili da kuma goyon bayan da ta nuna wa jam'iyar LP da Peter Obi, ɗan takarar shugaban kasa a 2023, sune suka sanya magoya bayan APC suka yi adawa da naɗinta.
A rahoton Western Post, mambobin APC, "sun nuna rashin gamsuwa ga manyan kusoshin gwamnati cewa bai dace a naɗa ƴar adawa ta yi aiki a babban bankin CBN ba."
Sakamakon haka ne, Shugaban Kasa Tinubu ya janye naɗin da ya mata tare da bukatar majalisar dattawa ta yi watsi da naɗin Onwudiwe.
Idan baku manta ba ranar Alhamis, 14 ga watan Maris, Bola Tinubu ya buƙaci majalisar dattawa ta amince da naɗin Onwudiwe a matsayin mambar majalisar daraktocin CBN.
Naɗin na kunshe a wata wasiƙa da ya aika zuwa ga shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, kuma ya karanta a zaman sanatoci na ranar Laraba.
Rikicin Ribas: Matasa sun zargi shugaban APC
A wani rahoton kuma matasan jihar Ribas sun yi ikirarin cewa shugaban APC, Cif Tony Okocha da wasu jiga-jigai na kulle-ƙullen kifar da Gwamnatin Simi Fubara.
Gamayyar ƙungiyoyin shugabannin matasan sun jaddada cewa a shirye suke su ruguza duk wani yunkuri na kawo cikas ga zaɓaɓɓiyar gwamnati.
Asali: Legit.ng