Cushen N3.7trn: Shugaban Majalisar Dattawa Zai Yi Murabus Saboda Kalaman PDP? An Bayyana Gaskiya

Cushen N3.7trn: Shugaban Majalisar Dattawa Zai Yi Murabus Saboda Kalaman PDP? An Bayyana Gaskiya

  • Majalisar dattawa ta mayar da martani ga jam'iyyar PDP kan kiran da ta yi na cewa Sanata Godswill Akpabio ya yi murabus
  • Shugaban kwamitin yaɗa labarai, Yemi Adaramodu, ya ce Akpabio ba zai sauka daga shugabancin majalisar dattawa ta 10 kamar yadda PDP ta buƙata ba
  • Ya ce babu wata ƙarya ko zarge-zarge mara tushe da zasu ɗauke hankalin majalisar wajen sauken nauyin da ƴan Najeriya suka ɗora mata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar dattawa, Sanata Yemi Adaramodu (APC, Ekiti ta kudu) ya mayar da martani ga babbar jam'iyyar adawa PDP.

Sanata Adaramodu ya caccaki jam'iyyar PDP kan kiran da ta yi cewa ya kamata shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya yi murabus, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan Ningi ya yi murabus, an naɗa sabon shugaban ƙungiyar sanatocin Arewa

Sanata Godswill Akpabio.
Akpabio ba zai yi murabus ba, kakakin majalisar dattawa ya mayar da martani ga PDP Hoto: NGRSenate
Asali: Facebook

Majalisa: PDP ta taso Akpabio a gaba

PDP ta buƙaci Akpabio ya yi murabus ne biyo bayan zargin cushen makudan kuɗi da suka kai N3.7trn a kasafin kuɗin 2024 kuma babu wani bayanin aikin da za a yi da su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bisa wannan zargin cushen kuɗin da ake ganin ya faru a ƙarƙashinsa, jam'iyyar PDP ta buƙaci Akpabio ya yi murabus daga kujerar shugaban majalisar dattawa.

Akpabio zai yi murabus daga shugaban majalisa?

Amma Adaramodu ya shaida wa manema labarai ranar Alhamis a Abuja, cewa Akpabio ba zai yi murabus ba saboda "bai aikata wani laifi da ya cancanci ya yi murabus ba."

A rahoton Leadership, Sanatan ya ce:

"Kiran da PDP ta yi na Sanata Godswill Akpabio ya yi murabus daga kujerar shugaban majalisar dattawa da abu ne mai yiwuwa ba kuma ya nuna jam'iyyar tana kokarin yaɗa karya da rashin ɗa'a.

Kara karanta wannan

"Har yanzu ni mamban jam'iyyar PDP ne" Ministan Tinubu ya yi magana kan sauya sheƙa zuwa APC

"Saɓanin ikirarin PDP na cewa an cusa N3.7trn a kasafin 2024 ba tare da nuna wani aiki da za a yi da su ba, kowa ya sani babu wani abu mai kama da haka a kasafin da majalisa ta amince kuma Bola Tinubu ya sa hannu.
"Babu wata karya da zarge-zargen karya da za su ɗauke hankalin majalisar dattawa ta 10 karkashin Akpabio wajen kafa kyawawan dokoki da sauke nauyin ‘yan Najeriya."

Yar'adua ya zama sabon shugaban NSF

A wani rahoton kuma Kungiyar sanatocin Arewa (NSF) ta naɗa Sanatan Katsina ta Tsakiya, Abdul'aziz Yar'adua a matsayin sabon shugabanta bayan Abdul Ningi ya yi murabus.

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ne ya sanar da haka a zaman majalisa na ranar Alhamis, 14 ga watan Maris.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262