Tinubu Ya Aike da Saƙo Majalisa, Ya Yi Sabon Muhimmin Naɗi a Babban Bankin Najeriya CBN

Tinubu Ya Aike da Saƙo Majalisa, Ya Yi Sabon Muhimmin Naɗi a Babban Bankin Najeriya CBN

  • Bola Ahmed Tinubu ya naɗa wanda zai maye gurbin Mista Kalu Eke, wanda ya ƙi karɓan tayin muƙami a babban bankin Najeriya (CBN)
  • Shugaba Tinubu ya roki majalisar dattawa ta amince da naɗin Dakta Ruby Onwudiwe a matsayin mamban majalisar daraktocin CBN
  • Sanata Godswill Akpabio, shugaban majalisar dattawa ne ya karanta wasiƙar da Tinubu ya turo a zaman sanatoci na ranar Laraba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi majalisar dattawan Najeriya ta amince da naɗin Dakta Ruby Onwudiwe, a matsayin darakta a CBN.

Shugaba Tinubu ya ɓukaci majalisar ta tantance tare da tabbatar da naɗinsa a matsayin mamban majalisar daraktocin babban bankin Najeriya (CBN), jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Abin sha'awa: Bola Tinubu ya yi buɗa baki 'Iftar' na azumin Ramadan tare da wasu gwamnoni a Villa

Shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Tinubu ya nada wanda zai maye gurbin Kalu Eke a CBN Hoto: Dolusegun16
Asali: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata wasiƙa da ya aika zuwa ga shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, kuma ya karanta a zaman sanatoci na ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya naɗa Onwudiwe ya canji Eke

A wasiƙar, Bola Tinubu ya ce bukatar tabbatar da naɗin ta yi daidai da tanadin sashe na 10, karamin sashe na daya na dokar kafa babban bankin Najeriya ta 2007, rahoton jaridar Gazette.

"Ina farin cikin gabatar da naɗin Dakta Ruby Onwudiwe ga majalisar dattawa domin tabbatar da shi a matsayin mamba a majalisar daraktoci ta babban bankin Najeriya (CBN).
"Ya kamata majalisar dattawa ta lura cewa Dakta Ruby Onwudiwe ne ya maye gurbin Mista Kalu Eke, saboda Mista Eke ya nuna ba zai ƙarɓi muƙamin ba.
“Saboda haka ina fata majalisar dattawa za ta duba tare da tabbatar da nadin Onwudiwe kamar yadda doka ta tanada."

Kara karanta wannan

Cushen N3.7trn: Shugaban majalisar dattawa zai yi murabus saboda kalaman PDP? An bayyana gaskiya

- Bola Ahmed Tinubu.

Nadin mukamai a bankin CBN

Idan ba ku manta ba, Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa Tinubu ya naɗa daraktoci biyar a CBN, amma mutum ɗaya daga Kudu maso Gabas ya ce ba zai karɓi muƙamin ba.

Bayan haka ne majalisar dattawan ta tabbatar da sauran mutane 4, tare da barin giɓin mutum ɗaya, wanda a yanzu Shugaba Tinubu ya maye gurbinsa.

Tinubu ya miƙa kasafin kudin FCTA a 2024

A wani rahoton kuma Bola Ahmed Tinubu ya aike da kasafin kuɗin 2024 na hukumar gudanarwa ta Abuja (FCTA) ga majalisar wakilan tarayya.

Shugaban ƙasar ya buƙaci majalisar ta hanzarta aiki kan kasafin kuma ta amince da shi, hakan na kunshe a wasiƙar da ya tura majalisar ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262