Ningi: Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Zargin Cushen N3.7trn a Kasafin Kuɗi 2024, BudgIT Ta Tona Gaskiya

Ningi: Sabbin Bayanai Sun Fito Kan Zargin Cushen N3.7trn a Kasafin Kuɗi 2024, BudgIT Ta Tona Gaskiya

  • Sabbin bayanai na kara fitowa kan cushe a kasafin kuɗin 2024 yayin da ƙungiyar BudgIT ta tabbatar da zargin Sanata Abdul Ningi
  • Sanata Ningi mai wakiltar Bauchi ta Tsakiya ya yi zargin cewa akwai wasu kuɗi N3.7trn da aka cusa a kasafin waɗanda babu bayani a kansu
  • Sai dai BudgIT ta bayyana yadda aka kasafta kuɗin da kuma zargin dakataccen Sanatan kan rashin cikakken bayani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Wata ƙungiyar farar hula mai zaman kanta da ke sa ido kan kasafin kuɗin Najeriya (BudgIT) ta tsoma baki kan zargin cushen N3.7trn a kasafin kuɗin 2024.

Ƙungiyar ta ayyana cikakken goyon bayanta ga ikirarin dakataccen Sanata Abdul Ningi, cewa an yi cushen sama da Naira tiriliyan 3 a kasafin na wannan shekara.

Kara karanta wannan

Arewa ta barke da murna bayan ware $1.3bn kan aikin layin dogo daga Kano zuwa Maradi

Sabbin bayanai na ƙara fitowa kan cushe a kasafin 2024.
BudgIT ta yi magana kan ikirarin Sanata Ningi na cusa N3.7trn Hoto: NGRSenate
Asali: Facebook

Daraktan kuma wanda ya kafa BudgIT, Seun Onigbinde, ne ya bayyana haka yayin wata hira da gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya jaddada cewa Ningi ya yi gaskiya kan batun cewa babu cikakken bayanin yadda za a kashe Naira tiriliyan 3.7 a cikin kasafin kudin shekarar 2024.

Cushen N3.7trn: Majalisa ta dakatar da sanata Ningi

Idan ba ku manta ba Legit Hausa ta kawo maku rahoton cewa majalisar dattawa ta dakatar da Ningi, Sanata mai wakiltar Bauchi ta tsakiya a ranar Talata.

An dakatar da sanatan ne bisa zargin da ya yi cewa an zartar da nau'i biyu na kasafin kudin 2024 a majalisar dokokin kasar, lamarin da bai yi wa sanatoci daɗi ba.

Sanatan wanda kuma shi ne shugaban kungiyar sanatocin Arewa (NSF), ya yi zargin cewa an cusa Naira tiriliyan 3 a kasafin kudin, kuma an yi watsi da Arewa a gwamnatin Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Ningi: Majalisa ta dauki mataki kan Sanatan da yayi zargin cushen N3tr a Kasafin 2024

BudgIT ta goyi bayan Sanata Ningi

Onigbinde ya ce kasafin da aka ware wa majalisar tarayya, ma'aikatar shari’a ta ƙasa (NJC), hukumar zabe (INEC), asusun tallafawa manyan makarantu TETFund da sauran su, ba su da cikakken bayani.

Ya kara da cewa jama’a na da ‘yancin sanin yadda ake kashe kudaden da aka ware wa hukumomin da aka ambata, cewar rahoton Daily Trust.

"Kusan Naira tiriliyan 2 na kasafin kudin da shugaban kasa ya gabatar an ware su ne a matsayin kasafin kamfanoni mallakar gwamnati.
"Saboda haka idan Sanata Ningi ya ce akwai kasafin N25trn, eh, wannan shi ne kasafin MDA, ya sha bamban da kasafin kudin kamfanoni mallakar gwamnati wanda aka kara a yanzu.
"Gaskiya ne cewa ya faɗi haka amma ba yana nufin muna gudanar da kasafin kuɗi daban-daban guda biyu ba."

- Seun Onigbinde.

Hukumomin da aka ware wa maƙudan kuɗin

Shugaban ƙungiyar ya ce ba ya ga kasafin kamfanoni mallakar gwamnati, akwai kuɗaɗen da aka ware wa hukumomi kamar INEC, NJC, TETFUND da kuma majalisar dokokin ƙasa.

Kara karanta wannan

An hargitse a Majalisa kan zargin Sanata Ningi, an fifita manyan Sanatoci wurin rabon kudi

Ya ƙara da cewa:

"Bai kamata a ware wa TETFUND wasu kuɗi ba, INEC na karɓan makudan kuɗi amma babu bayanin yadda ake amfani da su, haka ma ɓangaren shari'a NJC da ita kanta majalisar tarayya."
"Wadannan al’amura ne da ya kamata a fito da su fili, idan aka hada duka wadannan, za su kai kusan N3.5trn zuwa N3.7trn.
"Don haka, idan abin da shi (Ningi) ke son bin ba'asi kenan, to akwai abubuwan da ke cikin kasafin kudin waɗanda ba a yi cikakken bayani ba. Yana da gaskiya."

Ministan Abuja ya gana da sanatoci a majalisa

A wani rahoton kuma Majalisar dattawa ta shiga ganawar sirri da ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike kan tabarɓarewar tsaro wanda ya fara shiga kwaryar birnin.

Wike tare da kwamishinan ƴan sandan Abuja, Benneth Igwe, sun amsa gayyatar da majalisar ta aika masu a makonnin da suka shige.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262