Shugaba Tinubu Ya Naɗa Tsohon Shugaban PDP da Wasu Mutum 2 a Manyan Muƙamai

Shugaba Tinubu Ya Naɗa Tsohon Shugaban PDP da Wasu Mutum 2 a Manyan Muƙamai

  • Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Mista Felix Amaechi Obuah a matsayin shugaban hukumar AMMC
  • Mista Obuah shi ne tsohon shugaban babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa, PDP a reshen jihar Ribas wanda ya gabata
  • Shugaban ƙasa Tinubu ya kuma naɗa wasu mutum biyu da zasu jagoranci ma'aikatu karkashin hukumar gudanarwa ta Abuja (FCTA)

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, ya amince da naɗin mutum uku a matsayin shugabannin wasu ma'aikatu da ke karkashin hukumar gudanarwa ta Abuja (FCTA).

Mutanen da ministan birnin tarayya, Nyesom Wike, ya ba da shawarar naɗawa sun haɗa da Abdulkadir Zulkarfi, kodinetan sashin raya garuruwan Abuja.

Kara karanta wannan

Ramadan: Shugaba Tinubu ya halarci buɗe tafseer na alƙur'ani, ya aika saƙo ga Musulmin Najeriya

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Tinubu ya ci gaba da naɗe-naɗe.a gwamnatinsa Hoto: @OfficialABAT
Asali: Twitter

Sauran su ne, Mista Felix Amaechi Obuah, a matsayin kodinetan hukumar raya cikin birni (AMMC) da Oladiran Olufemi Akindele, kodinetan cibiyar zuba jari a ayyukan more rayuwa ta Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon shugaban PDP ya samu muƙami

Legit Hausa ta gano cewa Mista Obuah, shi ne tsohon shugaban PDP ta jihar Ribas.

Haka nan kuma jigon babbar jam'iyyar adawa ta ƙasa, Obuah, ya kasance tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ogba-Egbema-Ndoni a jihar mai arziƙin man fetur.

Obuah, ɗaya daga cikin yaran Nyesom Wike, yana cikin waɗanda suka nemi tikitin takarar gwamnan Ribas karkashin inuwar PDP a zaɓen 2023.

Amma ɗan kasuwan bai samu tikitin jam'iyyar PDP a zaben fitar da gwani ba saboda Wike ya goyi bayan Siminalayi Fubara, gwamna mai ci.

Tsohon hadimin shugaban ƙasa, Tolu Ogunlesi ne ya tabbatar da haka a shafinsa na manhajar X ranar Talata.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi wani sabon nadi mai muhimmanci, ya maye gurbin wanda ya Buhari ya nada

Ya rubuta a shafinsa cewa:

"An naɗa tsohon shugaban jam'iyyar PDP ta jihar Ribas wanda ya gabata, Felix Obuah a matsayin kodinetan hukumar AMMC.
"Ya kasance tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ogba–Egbema–Ndoni a jihar Ribas."

Tinubu ya naɗa sabon shugaban NIMASA

A wani rahoton kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗin tsohon kwamishina a jihar Legas, Dayo Mobereola a matsayin sabon shugaban hukumar NIMASA

Naɗin Mobereola ya biyo bayan saukar Bashir Jamoh wanda tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya naɗa kan muƙamin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262