Babbar Kotun Tarayya Ta Yanke Hukunci Kan Bidiyon 'Dalan' Tsohon Gwamnan Kano Ganduje

Babbar Kotun Tarayya Ta Yanke Hukunci Kan Bidiyon 'Dalan' Tsohon Gwamnan Kano Ganduje

  • Tsohon gwamnan jihar Kano kuma shugaban APC na ƙasa, Dakta Abdullahi Ganduje ya samu nasara kan bidiyon Dala a babbar kotun tarayya
  • Kotun mai zama a birnin Kano ta yanke hukuncin cewa hukumar yaƙi da rashawa ta Kano ba ta da ƙarfin ikon binciken Dr. Ganduje kan bidiyon
  • Mai shari'a Abdullahi Liman ya bayyana cewa laifin na cin hanci da ake zargin tsohon gwamnan laifi ne na ƙasa, AGF da EFCC ne za su iya kai shi kotu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Babbar kotun tarayya mai zama a birnin Kano ta yanke hukunci kan bidiyon dala na tsohon gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.

Kotun ta yanke hukuncin cewa hukumar karɓan korafe-korafen jama'a da yaƙi da rashawa ta Kano (PCACC) ba ta da ƙarfin ikon bincikar Ganduje kan bidiyon zargin karbar cin hancin Dala.

Kara karanta wannan

Mutane 12 sun mutu yayin da wasu sama da 20 suka ji raunuka a babban titin Zaria zuwa Kaduna

Tsohon gwamnan Kano, Dakta Abdullahi Ganduje.
Hukumar yaki da rashawa ta Kano ba ta da ikon binciken Ganduje - Kotu Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Facebook

Allƙalin kotun, mai shari'a Abdullahi Liman ne ya bayyana haka yayin yanke hukunci kan batun ranar Talata, 5 ga watan Maris, 2024, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce abin da ake zargin tsohon gwamnan laifi ne na ƙasa wanda Antoni Janar na tarayya (AGF) ko hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ke da ikon gurfanar da shi.

Mai shari’a Liman ya ce hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa ta Kano tana da iyaka wajen binciken tsohon gwamnan.

Bidiyon Dala: Zamu wuce kotun ɗaukaka kara - PCACC

Da yake jawabi ga manema labarai jim kaɗan bayan yanke hukunci, lauyan hukumar PCACC, Barista Usman Umar Fari, ya ce zasu yi nazari kan wannan hukunci.

Ya kuma tabbatar da cewa za su ƙalubalancin wannan hukunci a gaban kotun ɗaukaka ƙara, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Boko Haram: Sama da 90% na ainihin masu aƙidar ta'addanci sun mutu Inji Zulum

Ganduje: PCACC ta ɗauƙo babban lauya

A baya mun kawo muku rahoton cewa Hukumar yaki da cin hanci da karɓar korafe-korafe ta jihar Kano (PCACC), ta ce ta ɗauko hayar babban lauya Femi Falana.

Hukumar PCACC ta bayyana cewa Falana zai taimaka mata kan shari'ar da take yi da tsohon gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262