Shugaban INEC Ya Yi Nadamar Ayyana Tinubu a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben 2023? Gaskiya Ta Bayyana

Shugaban INEC Ya Yi Nadamar Ayyana Tinubu a Matsayin Wanda Ya Lashe Zaben 2023? Gaskiya Ta Bayyana

  • Gaskiya ta fito game da raɗe-raɗin cewa shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu, ya yi nadamar ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen 2023
  • Tinubu ya lallasa Atiku Abubakar na PDP da takwaransa na Labour Party, Peter Obi a zaɓen shugaban ƙasa da aka yi a ranar 25 ga watan Fabrairu
  • Wani shafin tantance gaskiya ya yi bincike kan iƙirarin cewa Yakubu ya yi nadamar ba Tinubu nasara duba da tsadar rayuwar da ake ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) na ƙasa, Farfesa Mahmud Yakubu na shan suka kan ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen 2023.

Wannan suka da ake wa Yakubu na zuwa ne yayin da ƴan Najeriya ke fama da wahalhalun rayuwa da yunwa waɗanda ake ganin gwamnatin Tinubu ce ta kawo su.

Kara karanta wannan

"Babu ruwan Tinubu" Minista ya fallasa ainihin waɗanda suka jefa ƴan Najeriya a wahala da yunwa

Shugaban INEC da Bola Tinubu.
Shugaban INEC da Bola Tinubu bayan cin zaben 2023 Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Tinubu: Karyar namadar Shugaban INEC

A yanzu kuma an fara yaɗa ikirarin cewa shugaban INEC ya fitar da wata sanarwa, wanda ta nuna nadamar ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya samu nasara a zaɓen.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sanarwan, an ce Yakubu ya ce ya yi da na-sanin gaggauta ba Tinubu nasara bayan ganin halin ƙuncin rayuwar da aka shiga a ƙasar nan.

Mafi yawan ƴan Najeriya a manhajar X suna ganin laifin shugaban INEC a wannan halin wahala da aka shiga karkashin mulkin Tinubu tun kafin ya cika shekara ɗaya.

Wane rahoto ne ake yaɗawa da sunan shugaban INEC?

A wani rahoto da Igbo Times Magazine ta wallafa, ya ce:

"Labari mai zafi: Na yi saurin ayyana Tinubu a matsayin shugaban ƙasa, ban taɓa tsammanin ƴan Najeriya za su shiga wahala ba - Shugaban INEC.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ministan Tinubu ya fadi dalili 1 da ya sa mutanen yankinsa ba za su yi zanga-zanga ba

"Shugaban INEC ya bayyana nadamar saurin ayyana Tinubu a matsayin shugaban Najeriya bayan ganin wahalar da mutane ke ciki.
"Shugaban hukumar zaɓe INEC ya fitar da sanarwa mai nuna nadamar da ya yi da bayyana Bola Tinubu a matsayin shugaban ƙasa a Najeriya."

Haka dai wannan ikirari na nadamar Mahmud Yakubu ke yawo a wasu shafuka da dama.

Farfesa Yakubu ya ayyana Bola Ahmed Tinubu na APC a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ranar Laraba, 1 ga watan Maris, 2023.

Menene gaskiyar wannan iƙirari?

Sai dai wata kafar tantance gaskiya, Africa Check, ta binciki ikirarin kuma ta lura a ranar Talata, 5 ga Maris, cewa ikirarin ya sabawa kalaman da Farfesa Yakubu ya yi a bainar jama'a game da zaben 2023.

Africa Check ta wallafa cewa:

"Duba da matsayin Yakubu, duk wata magana ko sanarwa da ya fitar dangane da zaɓen 2023 ƴan jarida ke yaɗawa, mun bincika mun gano babu wata kafar watsa labarai da ta buga wannan labarin.

Kara karanta wannan

"Ba zaku iya faɗa da ni ba" Shugaba Tinubu ya ɗau zafi, ya aike da saƙo mai ɗumi ga NLC

"Babu wata sanarwa mai kama da ikirarin a shafin yanar gizo na INEC ko wasu shafukan sada zumunta da ta saɓa wallafa aikace-aikacenta.
"Saboda haka ikirarin da ke yawo cewa Yakubu ya yi nadamar sanar da Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban kasa ƙarya ne."

- Africa Check

Gwamna ya naɗa korarrun ƴan majalisa a muƙamai

A wani rahoton kuma Mambobin majalisar dokokin jihar Filato guda 16 da kotun daukaka kara ta tsige sun samu muƙamai a gwamnatin Celeb Mutfwang.

Gwamnan ya naɗa su a matsayin jami'an hulɗa da jama'a a mazaɓunsu domin su taimaka masa wajen kawo ci gaba a faɗin jihar Filato.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262