"Babu Ruwan Tinubu" Minista Ya Fallasa ainihin Waɗanda Suka Jefa Ƴan Najeriya a Wahala da Yunwa

"Babu Ruwan Tinubu" Minista Ya Fallasa ainihin Waɗanda Suka Jefa Ƴan Najeriya a Wahala da Yunwa

  • Ministan ayyuka ya bayyana cewa babu ruwan Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu a halin tsadar rayuwar da ƴan Najeriya suka shiga
  • David Umahi ya bayyana cewa wasu abubuwa da Tinubu ya gada daga gwamnatocin baya ne suka kawo ƙarancin abinci
  • Sanata Umahi ya kuma yi iƙirarin cewa shugaban ƙasar ya fara warware dukkan matsalolin da suka jawo halin da aka shiga

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce bai kamata a zargi gwamnatin Bola Tinubu da laifin tabarbarewar tattalin arziki da ake fama da shi a kasar nan ba.

Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa ƴan Najeriya sun koka kan halin matsin tattalin arzikin da suka shiga sakamakon sauye-sauyen da gwamnati ta ɓullo da su.

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Ministan Tinubu ya fadi dalili 1 da ya sa mutanen yankinsa ba za su yi zanga-zanga ba

Ministan ayyuka, David Umahi.
Ba Tinubu ya kamata a zarga da kawo tsadar rayuwar da ake ciki ba, Umahi Hoto: David Umahi
Asali: Facebook

A watan Mayun 2023, Shugaba Tinubu ya sanar da ɗaukar wasu matakai na farfaɗo da tattalin arziki da suka hada da soke tallafin man fetur da kuma sakin Naira ta dogara da kanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shin Bola Tinubu ne ya jawo tsadar rayuwa?

Amma da yake zantawa da manema labarai ranar Lahadi a jihar Ebonyi, Umahi ya danganta wahalar da ake ciki da wasu abubuwan da suka gabata a tsohuwar gwamnati.

A cewarsa, gwamnatocin da suka shude sun haɗa tarin rigingimun manoma da makiyaya da dai sauran nau’ukan rashin tsaro wanda a cewarsa ya yi illa ga samar da abinci.

A kalamansa, ministan ayyukan ya ce:

"Ni ne shugaban kwamitin majalisar tattalin arziki ta kasa (NEC) kan magance rikicin manoma da makiyaya kuma na warware irin wadannan rikice-rikice a jihohi da dama musamman a Arewa.

Kara karanta wannan

Dattawa sun tsoma baki kan batun sojoji su kifar da Gwamnatin Shugaba Tinubu kan abu 2

"Waɗannan sulhu da aka yi sun haifar da sakamako mai kyau to amma tun farko matsalar ta yi illa ga harkar noma domin kanoma ba su iya zuwa gonakinsu.
"Ba zai yiwu a iya warware waɗannan tarin matsalolin cikin kanƙanin lokaci ba kuma ya kamata mu tambayi kanmu, taya za a magance su? Shugaba Tinubu na ƙoƙarin daƙile dukkan matsalolin."

- David Umahi

Umahi ya ce shiyyar Kudu maso Gabas ta tsira daga rikicin manoma da makiyaya wanda ke nuna Bola Tinubu ya magance babbar matsalar da ta zama alaƙaƙai a yankin, cewar rahoton Leadership.

Kwastam za ta dawo siyar da abinci a farashi mai rahusa

A wani rahoton kuma Yayin da ake cikin wani hali na matsin rayuwa a Najeriya, hukumar Kwastam za ta sake raba shinkafa a karo na biyu.

Hukumar ta ce Gwamnati ta ba da damar sake rabon shinkafar da aka kwace a hannun jama'a da suke kokarin fitar da ita ba Bbisa ka'ida ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262