Dattawa Sun Tsoma Baki Kan Batun Sojoji Su Kifar da Gwamnatin Shugaba Tinubu

Dattawa Sun Tsoma Baki Kan Batun Sojoji Su Kifar da Gwamnatin Shugaba Tinubu

  • Dattawan jihar Ekiti sun yi zaman gaggawa, sun faɗi matsayarsu kan masu kira ga sojoji su kifar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu
  • A wata sanarwa da suka fitar bayan kammala taron, sun ce babu cikakken ɗan Najeriya mai kishin ƙasa da zai so sauya gwamnati ba bisa ƙa'ida ba
  • Sun kuma yi kira ga Shugaba Tinubu ya gaggauta shawo kan halin tsadar rayuwar da mutane ke ciki tun kafin tura ta kai bango

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Ekiti - Ƙungiyar dattawan jihar Ekiti ta yi Allah wadai da masu kiraye-kirayen sojoji su kifar da gwamnati mai ci saboda taɓarɓaarewar tsaro da matsin tattalin arziƙi.

Amma duk da haka dattawan sun yi kira ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya gaggauta ɗaukar matakan warware matsalolin tattalin arziki da tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

"Mu ba ƴan siyasa bane" Ƴan ƙwadago sun maida zazzafan martani kan kalaman Shugaba Tinubu

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu.
Dattawan Ekiti Sun Caccaki Nasu Kiran a Yi Juyin Mulki a Najeriya Hoto: NGRPresident
Asali: Facebook

A cewarsu, halin da ƴan Najeriya suka tsinci kansu na yunwa da tsadar kayan amfanin yau da kullum na neman kai wa maƙura, kamar yadda Leadership ta rahoto.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sun kuma yabawa Shugaba Tinubu bisa yunƙurin aiwatar da rahoton Oronsaye na 2012, inda suka roƙi kar ya tsaya ɓata lokaci kan wasu batutuwa da ake ta cece kuce kamar ƴan sandan jihohi.

Dattawan sun cimma wannan matsaya ne a wurin taron gaggawa da suka gudanar a Ado Ekiti, babban birnin jihar Ekiti.

Menene hangen dattawan kan juyin mulki?

Manyan ‘yan kasar sun ce irin wadannan kalamai (neman a kifar da gwamnatin Tinubu) na iya haifar da rikici tare da mayar da kasar baya shekaru masu yawa.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar dattawan jihar, Farfesa Joseph Oluwasanmi da babban sakatare, Niyi Ajibulu suka sanya wa hannu.

Kara karanta wannan

Gwamnan Arewa ya roƙi Shugaba Tinubu ya taimaka masa a ƙoƙarinsa na kawo ƙarshen ƴan bindiga

Sanarwan ta ce:

"Dattawa sun yi tir da kalaman wasu ‘yan Najeriya wadanda ba wai kawai suna zagon kasa ga ofishin shugaban kasa ne ba, har ma da tunzura jama’a da kiraye-kirayen a sauya gwamnati ba bisa ka’ida ba.
"Muna gargaɗin duk wani basarake ko babban mutum mai faɗa a ji wanda kalamansa ko ayyukansa ke nuna yana bayan sojoji su kifar da gwamnati ya sauya tunani.
"Babu wani cikakken ɗan Najeriya mai kishin ƙasa da zai goyi bayan yunƙurin tarwatsa ƙasar nan."

Ƴan kwadago sun aike da saƙo ga Tinibu

A wani rahoton na daban Ƙungiyar TUC ta mayar da martani ga shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu kan kalaman da ya yi game da zanga-zangar ƴan kwadago.

Bola Tinubu ya caccaki kungiyoyin kwadago, yana mai cewa idan mulki suke so su jira 2027, kuma ya ce ba su kaɗai ne muryar ƴan Najeriya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262