Zaben Gwamnan Edo: Manyan 'Yan Takara 3 Daga APC, PDP da LP

Zaben Gwamnan Edo: Manyan 'Yan Takara 3 Daga APC, PDP da LP

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Benin City, Jihar Edo - Manyan jam’iyyun siyasa uku, APC, PDP da kuma Labour Party (LP) sun gudanar da zaɓukansu na fidda gwani tare da gabatar da ƴan takararsu na zaɓen gwamna da ke tafe a jihar Edo.

A cewar INEC, zaɓen gwamnan jihar Edo wanda zai maye gurbin Gwamna Godwin Obaseki zai gudana ne a ranar 12 ga watan Oktoba, 2024.

Zaben gwamnan jihar Edo
Ighodalo da sauran 'yan takara na son maye gurbin Obaseki Hoto: Asue Ighodalo/Journalist KC/Olumide Akpata
Asali: Facebook

Wa'adin mulkin Obaseki na biyu zai ƙare ne a ranar 11 ga Nuwamban 2024.

Yayin da mazauna jihar da masu kaɗa ƙuri’a ke dakon fara yaƙin neman zaɓe da kuma yadda za a kaɗa ƙuri’a, waɗannan su ne manyan ƴan takara a zaɓen gwamnan Edo a 2024, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya fusata ya caccaki hukumar INEC kan abu 1

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanata Monday Okpebolo (APC)

Gwamnan jihar Cross Rivers, Bassey Otu, shugaban kwamitin shirya zaɓen fidda gwanin na APC, ya bayyana Sanata Okpebolo a matsayin wanda ya lashe zaɓen bayan ya tattara sakamakon zaɓen ƙananan hukumomi 18.

  • Ranar haihuwa

An haifi Sanata Monday Okpebolo ne a ranar 12 ga watan Yuni, 1962. Ɗan siyasar mai shekaru 61 ya fito ne daga Uromi, ƙaramar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas ta jihar Edo.

Sanatan dai yana wakiltar mazaɓar Edo ta Tsakiya a majalisar dattawa dake Abuja.

  • Karatu

Ya yi karatunsa a makarantar firamare ta Uromi da sakandare a makarantar Uromi Grammar School.

Okpebholo ya yi digirin farko a fannin tattalin arzikin noma a shekarar 1986 da kuma digiri na biyu a fannin gudanar da gwamnati a shekarar 1990 dukkansu daga jami’ar Benin (UNIBEN).

Kara karanta wannan

Mataimakin gwamna ya ƙara haddasa sabuwar rigima a jam'iyyar PDP kan muhimmin abu 1

Asue Ighodalo (PDP)

Ighodalo ya samu ƙuri'u 577 a matsayin dan takarar jam'iyyar PDP a zaɓen fidda gwanin gwamnan jihar Edo da aka gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba.

  • Ranar haihuwa

An haifi Asue Ighodalo a ranar 19 ga watan Yuli, 1959. Ɗan kasuwan mai shekara 64 ya fito ne daga Okaigben, Ewohimi, a ƙaramar hukumar Esan ta Kudu maso Gabas a jihar Edo.

  • Karatu

Ɗan takarar gwamnan na PDP ya yi karatunsa na sakandare a babbar makarantar King’s College da ke Legas.

Ighodalo ya samu digirinsa na farko a fannin tattalin arziƙi a jami'ar Ibadan (UI) a shekarar 1981.

Ya samu LL.B Hons a makarantar tattalin arziki da kimiyyar siyasa ta London a 1984.

Ya kammala makarantar shari'a ta Najeriya a shekarar 1985.

Olumide Akpata (LP)

Mataimakin gwamnan jihar Abia, Ikechukwu Emetu, shugaban zaɓen fidda gwanin jam'iyyar Labour Party na Edo, ya bayyana Akpata a matsayin wanda ya lashe zaɓen fidda gwani na jam'iyyar.

Kara karanta wannan

Edo: Bayan matsalar da aka samu, APC ta bayyana wanda ya lashe tikitin takarar gwamna

  • Ranar haihuwa

An haifi Olumide Osaigbovo Akpata a ranar 7 ga watan Oktoba, 1972 a jihar Edo.

  • Karatu

Lauyan mai shekaru 51 ya samu shaidar kammala karatun digiri a fannin shari'a daga jami'ar Benin (UNIBEN) Edo a shekarar 1992.

Ya zama cikakken lauya a shekarar 1993.

Shaibu Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwanin Gwamna a Edo

A wani labarin kuma, kun ji cewa Phillip Shaibu, mataimakin gwamnan jihar Edo, ya lashe zaben fidda gwani na jam'iyyar PDP na gwamnan jihar Edo na 2024.

Shaibu ya lashe zaben fidda gwanin ne da ƙuri'u 301 yayin da dayan tsagin na Gwamna Godwin Obaseki na jam'iyyar bai gudanar da nasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng