Babbar Kotun Tarayya Ta Ɗauki Mataki Kan Tsohon Gwamnan Arewa da Ake Zargi, Ta Kafa Sharuɗda
- Bayan shafe kusan mako guda a hannun EFCC, tsohon gwamnan Kwara ya samu beli a babbar kotun tarayya mai zama a Ilorin ranar Jumu'a
- Kotun ta amince da buƙatar bayar da belin Abdulfatahi Ahmed kan kudi Naira miliyan 50 da mutum biyu da zasu tsaya masa
- Haka nan kuma ta umarci tsohon gwamnan ya miƙa fasfo ɗinsa na tafiye-tafiya da ƙarin wasu sharuɗɗa, duk bayan EFCC ta gurfanar da shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kwara - Babbar kotun tarayya mai zama a Ilorin ta bayar da belin tsohon gwamnan jihar Kwara, Alhaji Abdulfatahi Ahmed, kan kuɗi Naira miliyan 50.
Kamar yadda The Nation ta ruwaito, tsohon gwamnan zai gabatar da mutum biyu da zasu tsaya kuma dole ya kasance sun mallaki kadarori a Ilorin, babban birnin jihar Kwara.
Tsohon gwamnan ya shafe kwanaki a hannun EFCC
Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta gurfanar da Ahmed a gaban babbar kotun tarayya yau Jumu'a, 23 ga watan Fabrairu, 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tun ranar Litinin da ta gabata, Ahmed ya kai kansa ofishin EFCC na Ilorin biyo bayan gayyatar da aka masa, inda hukumar ta tsare shi har zuwa yau da ta gurfanar da shi.
Abdulfatahi Ahmed zai kuma mika wa kotun fasfo ɗinsa na tafiye-tafiya duk a cikin sharuɗɗan belin da aka amince masa, kamar yadda Channels tv ta rahoto.
Wace tuhuma EFCC take wa Ahmed?
EFCC na zargin tsohon gwamnan da karkatar da wasu makuɗan kuɗi da suka kai Naira biliyan 10 a lokacin da yake kan kujerar mulkin jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiya.
Ahmed, ya jagoranci jihar na tsawon shekaru takwas daga watan Mayu na shekarar 2011 zuwa watan Mayu, 2019, inda ya miƙa mulki ga gwamnan yanzu na APC.
Abinda ya faru lokacin gurfanar da tsohon gwamnan Kwara
A wani rahoton kuma mun kawo muku yadda jami'an tsaro suka hana ƴan jarida shiga kotu yayin da aka gurfanar da tsohon gwamna, Abdulfatahi Ahmed.
Sakataren watsa labaran tsohon gwamnan ya nuna rashin jin daɗinsa kan abinda ya kira shari'ar sirri da ake shirin yi wa mai gidansa
Asali: Legit.ng