Hukumar EFCC Ta Gurfanar da Tsohon Gwamnan Arewa a Gaban Babbar Kotu, Bayanai Sun Fito

Hukumar EFCC Ta Gurfanar da Tsohon Gwamnan Arewa a Gaban Babbar Kotu, Bayanai Sun Fito

  • A ƙarshe dai hukumar yaƙi da marasa gaskiya EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatahi Ahmed a gaban babbar kotun tarayya
  • Rahotanni sun nuna cewa jami'an ƴan sanda sun hana ƴan jarida shiga harabar kotun domim ɗaukar shari'ar ranar Jumu'a
  • Sakataren watsa labaran tsohon gwamnan ya nuna rashin jin daɗinsa kan abinda ya kira shari'ar sirri da ake shirin yi wa mai gidansa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kwara - Hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kwara, Abdulfatahi Ahmed a gaban kotu.

Kamar yadda Channels tv ta tattaro, EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan ne a gaban babbar kotun tarayya mai zama a Ilorin ranar Jumu'a, 23 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Murna ta ɓarke yayin da gwamnan APC ya fara siyar da shinkafa kan farashi mai rahusa ga talakawa

EFCC ta gurfanar da tsohon gwamnan Kwara, Abdulfatahi Ahmed.
Hukumar EFCC Ta Gurfanar da Tsohon Gwamnan Kwara, Ahmed a Gaban Kotu Hoto: Alhaji Abdulfatahi Ahmed, EFCC
Asali: Facebook

Sai dai an hana ƴan jarida ɗaukar zaman shari'ar Abdulfatah Ahmed yayin da aka hana su shiga zauren da kotun ke zama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadimin Ahmed ya koka kan shari'ar

Da yake zantawa da manema labarai a harabar kotun, babban sakataren watsa labaran tsohon gwamnan, Wahab Oba, ya koka kan abinda ya kira shari'ar sirri da ake wa Ahmed.

Ya kuma bayyana cewa wannan shari'ar ba komai bace illa siyasa, inda ya ƙara da cewa:

"Hukumar EFCC za ta gurfanar da tsohon Gwamna Dakta Ahmed a gaban kuliya don haka mun zo mu shaida yadda za a fara shari’ar.
"A ƙa'ida kotu wuri ne na kowa da kowa, don haka damuwar mu kawai ita ce a yi wannan shari'a a buɗe kowa ya ga yadda zata wakana.
"Mun gaza fahimtar dalilin da ya sa ƴan sanda suka hana musamman ƴan jarida shiga domin ɗaukar rahoton shari'ar."

Kara karanta wannan

Babbar kotun tarayya ta ɗauki mataki kan tsohon gwamnan Arewa da ake zargi, ta kafa sharuɗda

Meyasa EFCC ta kama tsohon gwamnan?

Hukumar yaki da cin hanci EFCC ta kama Ahmed ranar Litinin, inda jami'ai suka titsiye shi da tambayoyi kan ɓatar biliyoyin Naira a lokacin da yake gwamnan jihar.

Ahmed ya riƙe kujerar gwamnan jihar Kwara da ke Arewa ta Tsakiya tsakanin watan Mayun 2011 zuwa Mayu 2019 kafin ya mikawa Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq, Sahara Reporters ta ruwaito.

Kwana nawa Ahmed ya shafe a hannun EFCC?

A wani rahoton kuma mun kawo muku yadda EFCC ta riƙe tsohon gwamnan Kwara tun da ƴa miƙa kansa a ofishinsu da ke Ilorim, babban birnin jihar Kwara.

Bayanai sun nuna cewa hukumar ta gayyaci Ahamed domin ya amsa tambayoyi kan zargin karkatar da wasu kudi N10bn a lokacin mulkinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262