Mata Sun Fito Kan Tituna Zanga-Zanga, Sun Aike da Muhimmin Saƙo Ga Ministan Tinubu
- Gwamna Sim Fubara ya samu gagarumin goyon baya daga mata a jihar Ribas yayin da yake fama da rikicin siyasa mai zafi
- Dandazon matan da suka haɗa fitattun jaruman Nollywood, sun fito tattaki a wurare masu muhimmanci bayan kalaman ministan Abuja kan zaɓen 2027
- Matan da suka gudanar da zanga-zangar sun yi kira ga ƴan siyasar jihar Ribas su bar Gwamna Fubara ya gudanar da mulki cikin kwanciyar hankali
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Rivers - Dandazon mata daga ƙananan hukumomi 23 na jihar Ribas sun fantsama kan tituna a Fatakwal, babban birnin jihar ranar Alhamis, 22 ga watan Fabrairu.
Matan sun fito wannan zanga-zanga ne domin sake jaddada mubaya'a da goyon bayan Gwamna Siminalayi Fubara yayin da rikicin siyasa ya dabaibaye jihar Ribas, Punch ta rahoto.
Idan baku manta ba ministan birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya zaɓo tare da yin aiki tukuru har Fubara ya samu nasara a zaben gwamna na watan Maris.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai watanni shida bayan Fubara ya ɗare kan madafun iko, ya raba gari da uban gidansa na siyasa kuma tun wannan lokacin suke zaman doya da manja.
Matan sun aika saƙo ga Wike da wasu ƴan siyasa
Amma a yau Alhamis, masu ruwa da tsaki ƙarƙashin kungiyar matan da ke tare da Sim, sun fito tattaki tun daga mahaɗar CFC a titin Aba har zuwa Polo Club a Fatakwal.
Mstan waɗanda suka sanya fararen riguna da huluna masu launin ja da kore sun riƙa tiƙa rawa suna wakoki yayin wannan tattaki, kana sun ɗaga kwalaye masu rubutu daban-daban.
Wasu daga cikin abinda aka rubuta a kwalayen sun haɗa da, "ku bar Fubara ya yi mulki cikin natsuwa," "Allah ya bamu zaman lafiya a Ribas," "Iyaye mata suna son zaman lafiya," da sauransu.
Shugaban majalisar dattawa ya tona asirin masu ɗaukar nauyin zanga-zanga kan tsadar rayuwa a jihohi 4
Wata yar wasan barkwanci, Julius Agwu, jaruma a masana'antar Nollywood da shugabar LP ta jihar, Hilda Dokubo, na daga cikin manyan matan da suka shiga tattakin.
Jam'iyyar APC Ta Samu Ƙarin Ƴan Majalisu Biyu
A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta samu ƙarin ƴan majalisu a zauren majalisar dokokin jihar Delta bayan kammala zaben cike gurbi
Hakan ya biyo bayan rantsar da ƴan majalisu biyu da suka samu nasara a kotun ɗaukaka ƙara da kuma zaɓen cike gurbi a inuwar APC
Asali: Legit.ng