Ganduje Ya Kira Taron Gaggawa Domin a Magance Wutar da Aka Huro a Jam’iyyar APC

Ganduje Ya Kira Taron Gaggawa Domin a Magance Wutar da Aka Huro a Jam’iyyar APC

  • Shugabannin APC na kasa a karkashin jagorancin Abdullahi Umar Ganduje sun yi zaman gaggawa a yammacin ranar Talata
  • ‘Yan majalisar NWC a jam’iyyar APC suna kokarin shawo kan rikicin da aka shiga a dalilin tsaida ‘dan takaran gwamnan Edo
  • Bayan zaman da Abdullahi Ganduje yayi da sauran shugabanni na kasa, an amince zaben tsaida gwanin bai kammala ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - Majalisar gudanarwa ta kasa watau NWC a jam’iyyar APC tayi zama na gaggawa a game da abubuwan da ke faruwa.

Zaben tsaida ‘dan takaran gwamna a jihar Edo ya kawo rigima a APC, saboda haka Daily Trust ta ce NWC ta kira taron gaggawa.

Taron APC
Abdullahi Ganduje ya shirya taro a APC Hoto: Abdullahi Umar Ganduje PhD OFR
Asali: Facebook

Abdullahi Ganduje ya zauna da APC NWC

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta shiga rudani bayan ayyana zaben fidda gwanin Edo 'Inconclusive', ta fadi dalili

Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya jagoranci wannan taro a sakatariyar APC a matsayinsa na shugaban jam’iyya mai mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majiya ta bayyana cewa taron bai rasa nasaba da abubuwan da suka biyo bayan zaben tsaida gwanin da APC ta shirya a Edo.

Jam'iyyar APC tana da 'yan takara 3 a Edo

Kuna da labarin yadda aka tashi da ‘yan takara uku a dalilin rabuwar kai a jam’iyyar APC.

An rasa wanene ainihin ‘dan takaran APC a zaben sabon gwamna da za ayi domin a gaji kujerar Godwin Obaseki a Satumban bana.

Hon. Anamero Dekeri ya dura sakatariyar APC inda ya bukaci jam’iyya ta ba shi takardar shaidar lashe zaben da aka gudanar.

Kwamitin gwamna Hope Uzodimma da NWC ta tura ya ce Hon. Dennis Idahosa ne ya lashe zaben ‘dan takaran da aka shirya a APC.

Kara karanta wannan

Edo 2024: Dirama yayin da 'dan takarar APC ya dira ofishin Ganduje, ya gabatar da bukata 1 tak

An samu wasu ‘yan taware da suka yi na su zaben a gidan Fasto Osagie Ize-Iyamu, a karshe aka bada tikiti ga Monday Okpebholo.

APC ba ta kammala zaben gwani a Edo ba

Bayan taron ne aka samu labarin cewa zaben tsaida gwanin jihar Edo bai kammala ba, har yanzu akwai aiki a gaban majalisar NWC.

NWC a karkashin jagorancin Abdullahi Ganduje za ta nemi yadda za ta warware matsalar.

Siyasar Edo tana ba APC ciwon kai

Osagie Ize-Iyamu ya yi takarar gwamnan Edo a karkashin PDP da APC a 2016 da 2020, wannan karo sai aka ji labari ya fasa takara.

Ana kishin-kishin cewa Sanatan Edo ta Arewa kuma tsohon shugaban APC, Adams Oshiomhole bai tare da Ize-Iyamu a wannan karo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng