Shugaba Tinubu Ya Yi Muhimmin Abu 1 Jim Kaɗan Ya Dawo Daga Birnin Adis Ababa
- Jim kaɗan bayan ya dawo daga ƙasar Habasha, Bola Ahmed Tinubu, ya yi sabon naɗi da zai sauya akalar manyan makarantu a ƙasar nan
- Shugaban ƙasar ya naɗa tsohon darakta janar na NYSC, Suleiman Kazaure a matsayin shugaban kwamitin yaƙi da munanan ayyuka a manyan makarantu
- Sunday Asefon, mai taimaka wa shugaban ƙasa kan hulɗa da ɗalibai ne ya sanar da haka ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu, 2024
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da kaddamar da wani kwamiti na musamman da zai yi yaki da munanan ayyuka a manyan makarantun kasar nan.
Babban mai taimakawa shugaba Tinubu na musamman kan huldar dalibai, Sunday Asefon, ne ya sanar da hakan a ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu.
A rahoton The Nation, shugaban ƙasar ya naɗa tsohon shugaban hukumar kula da matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC), Manjo Janar Suleiman Kazaure mai ritaya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon Darakta Janar na NYSC, Kazaure, zai jagoranci sabon kwamitin wanda zai maida hankali wajen kawar da munanan ɗabi'u a manyan makarantu (SESV-TI).
Neyasa Tinubu ya kafa kwamitin?
Asefon ya ce wannan wani muhimmin mataki ne na magance matsaloli da nuna damuwar ƴan Najeriya dangane da wasu abubuwa da ke faruwa a manyan makarantun kasar nan.
Wannan sanarwar ta zo ne jim kadan bayan da shugaba Bola Tinubu ya koma birnin Abuja daga taron kungiyar tarayyar Afirka wanda aka yi a Addis Ababa na kasar Habasha.
A wata sanarwa da ya fitar, Asefon ya ce shan miyagun kwayoyi, kungiyoyin asiri, damfarar yanar gizo, cin zarafi da cin mutuncin ilimi, da sauransu, na cikin munanan dabi’un da ke kawo cikas a harkar ilimi da ci gaban dalibai.
A ruwayar PM News, ya ce:
"Kafa wannan kwamiti na musamma ya nuna ƙoƙarin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, wajen cika alƙawarinsa na kare makomar ɗaliban Najeriya."
Ƴan kwadago sun gindaya sabbin sharuɗɗa
A wani rahoton kuma Ƴan kwadago zasu zauna da wakilan gwamnatin tarayya ranar Litinin, 19 ga watan Fabrairu, 2024 kan batun tsadar rayuwa da albashi.
Wannan taro na zuwa ne yayin da ƙungiyar kwadago (NLC) ta ƙasa ke shirin tsunduma yajin aiki a ƙarshen watan da muke ciki.
Asali: Legit.ng