Shugaba Tinubu Ya Naɗa Mutum 5 a Manyan Muƙamai a Babban Banki CBN, Ya Tura Saƙo Majalisa
- Bola Ahmed Tinubu ya aike da sunayen mutum 5 da ya naɗa a matsayin daraktoci a babban bankin Najeriya (CBN) ga majalisar dattawa
- Sanata Godswill Akpabio, ya karanta sunayen mutanen ga sauran sanatoci a zaman majalisar na ranar Talata a Abuja
- A wata wasiƙar ta daban kuma, shugaban kasar ya nemi majalisar ta amince da naɗin kwamishinan NPC mai wakiltar jihar Osun
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya buƙaci majalisar dattawan Najeriya ta tantance tare da amincewa da mutane biyar da ya naɗa a babban bankin Najeriya (CBN).
Tinubu ya roƙi majalisar ta amince da naɗin mutane biyar a matsayin daraktocin majalisar gudanarwa ta CBN, kamar yadda The Nation ta ruwaito.
Wannan na ƙunshe a wata wasika da shugaban ƙasar ya aike ga shugaban majalisar, Sanata Godswill Akpabio, kuma ya karanta a zaman yau Talata, 13 ga watan Fabrairu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani ɓangaren wasiƙar wanda Akpabio ya karanta ya ce:
"Bisa ga tanadin sashe na 6, karamin sashe na 1b da sashe na 10 karamin sashe na 1 da na 2 na dokar kafa babban bankin Najeriya na shekarar 2007.
"Ina farin cikin gabatar da sunayen mutane biyar ga majalisar dattawa domin tabbatar da su a matsayin daraktocin majalisar gudanarwa ta babban banki CBN.
"Sunayen waɗanda na naɗa sun haɗa da Robert Agbide, Ado Wanga, Muritala Sagaley, Urom Eke da kuma Olayinka Aliyu. Ina fatan majalisa zata duba wannan buƙata."
Bayan nan ne Sanata Akpabio ya miƙa sunayen mutanen ga kwamitin majalisar kan harkokin banki, inshora da sauran cibiyoyin hada-hadar kuɗi domin ɗaukar mataki na gaba.
Tinubu ya naɗa kwamishinan NPC
Bugu da kari a wata wasiƙa ta daban, Tinubu ya bukaci majalisar ta tabbatar da nadin Mista Hamidu Rahim a matsayin kwamishinan hukumar kidaya ta kasa (NPC) mai wakiltar jihar Osun.
Shugaba Tinubu ya ce ya yi wannan naɗi ne bisa tanadin sashe na 154 karamin sashe na 1 na kundin tsarin mulkin 1999 (wanda aka yi wa gyara), cewar rahoton Premium Times.
Sanata Akpabio ya miƙa wannan bukata ga kwamitin kula da kidayar ƴan Najeriya da katin shaida na ƙasa domin yin aiki na gaba ya dawo da rahoto a mako ɗaya.
An rantsar da sabbin sanatoci 3 a majalisar
A wani rahoton Majalisar dattawan Najeriya ta rantsar da sabbin sanatoci uku a zamanta na yau Talata, 13 ga watan Fabrairu, 2024 a birnin tarayya Abuja.
Sanata Godswill Akpabio ne ya jagoranci rantsar da sanatocin da misalin ƙarfe 11:41 na safe kuma daga bisani aka nuna musu wurin zamansu.
Asali: Legit.ng