Abu Ya Girma: Ƴan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Kan Sanatan APC, Sun Tafka Ɓarna Mara Daɗi

Abu Ya Girma: Ƴan Bindiga Sun Kai Mummunan Hari Kan Sanatan APC, Sun Tafka Ɓarna Mara Daɗi

  • Miyagun ƴan bindiga sun kai hari gidan sanatan Imo ta Arewa, Sanata Patrick Ndubueze ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairu, 2024
  • Rahotanni daga majiya mai ƙarfi sun nuna cewa Sanatan ya tsallake rijiya da baya a harin wanda aka yi nufin halaka shi
  • Duk da Sanata Ndubueze ya yi nasarar tsira da rayuwarsa, ɗan sandan da ke ba shi tsaro ya rasa ransa bayan samun munanan raunuka

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Imo - Ƴan bindigan sun farmaki Sanata mai wakiltar jihar Imo ta Arewa (Shiyyar Okigwe), Sanata Patrick Ndubueze, inda suka halaka ɗaya daga cikin dogaransa.

Wata majiya da ke kusa da Sanatan ta shaida wa jaridar The Nation cewa ‘yan bindigar sun kai farmaki gidan Sanatan ne da safiyar ranar Litinin, 12 ga watan Fabrairu.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Amarya ta hallaka mijinta a jihar Neja

Sanata Patrick Ndubueze.
Sanatan Jihar Imo Ya Sha Kyar a Mummunan Harin Yan Bindiga, An Kashe Dogari Hoto: @Davidsoffor
Asali: Twitter

Ƴan bindigan sun kashe ɗan sanda ɗaya

Majiyar ta bayyana cewa sanatan ya samu nasarar tsallake rijiya da baya, ya tsira ba tare da jin rauni ba amma maharan sun bindige ɗaya daga cikin ƴan sanda da ke ba shi tsaro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Muttumin ya ce:

"Labarin cewa ƴan bindiga sun farmaki Sanata Patrick Ndubueze, gaskiya ne, sun kutsa kai gidansa da ke Umualumoke kuma sun kashe ɗan sanda da yake aiki da shi a matsayin dogari.
"Tabbas sun kai hari gidansa sun halaka jami'in ɗan sanda ɗaya. Mai yuwuwa ƴan bindigan da suka kai masa harin ne suka farmaki gidan gyaran halin Okigwe, suka saki wasu fursunoni.
"Sun kuma tafi da jami'in hukumar gyaran hali guda ɗaya. Okigwe ta zama filin yaƙi domin babu wanda ya tsira, muna rayuwa ne cikin tsoro, mafi akasarin matasan mu sun tsere saboda fargabar kada a kashe su."

Kara karanta wannan

Babbar magana: Tsagerun ƴan bindiga sun kashe fitaccen lauya a Najeriya

Ya kuma koka cewa duk da akwai jami'an tsaro sosai a yankin amma ba su tabuka komai da nufin magance matsalar hare-haren waɗannan ƴan ta'adda.

Sanata Ndubueze na jam'iyyar APC ya samu nasarar zama mamban majalisar dattawa bayan lashe zaɓen Imo ta Arewa ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023.

Wane mataki jami'an tsaro suka ɗauka?

Jami'in hulɗa da jama'a na rundujar ƴan sandan jihar, Henry Okoye, ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda Daily Post ta ruwaito.

Ya ce kwamishinan ƴan sanda, Aboki Danjuma, ya tashi tawagar dakaru na musamman da zasu farauto maharan duk inda suka shiga.

An kashe ƴan kasuwa 9 a Katsina

A wani rahoton kuma Yan bindiga sun halaka ƴan kasuwa 9 a kan hanyar komawa gida bayan tashi daga kasuwar Jibia ranar Lahadi da yamma.

Mazauna yankin sun bayyana cewa maharan sun kuma ƙona motoci biyu da ƴan kasuwar ke ciki kuma ana zargin sun yi garkuwa da wasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262