Gwamnoni Sama da 6 Sun Sa Labule Kan Muhimmin Abu 1 da Ya Shafi Ƴan Najeriya, Bayanai Sun Fito

Gwamnoni Sama da 6 Sun Sa Labule Kan Muhimmin Abu 1 da Ya Shafi Ƴan Najeriya, Bayanai Sun Fito

  • Gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya sun fara yunƙurin lalubo hanyar tsamo mutane daga kangin tsadar rayuwa da yunwa
  • A yau Litinin, 12 ga watan Fabrairu, 2024 gwamnini suka haɗu a birnin tarayya Abuja domin tattauna halin da ƙasar nan ke ciki
  • Bayanai sun nuna cewa akalla gwamnoni 6 ne suka halarci zaman wanda ke gudana yanzu haka a masaukin gwamnan jihar Oyo da ke Asokoro

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Gwamnonin da suka samu nasarar ɗarewa kan madafun iko karƙashin inuwar Peoples Democratic Party (PDP) na ganawa yanzu haka a birnin Abuja.

Gwamnonin jam'iyyar PDP sun shiga wannan zama ne domin tattaunawa kan halin da ƙasar nan ke ciki yayin da mutane ke fama da tsadar rayuwa.

Kara karanta wannan

Gwamnoni ga Tinubu: Ga hanyar shawo kan matsalar tsadar abinci da tattalin arziki

Gwamnonin PDP sun sa labule a Abuja.
Gwamnonin Jam'iyyar PDP Sun Sa Labule a Abuja kan muhimmin batu Hoto: PDP
Asali: Facebook

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rahoto, wannan taro na gudana yanzu haka a masaukin gwamnan jihar Oyo da ke Anguwar Asokoro a babban birnin tarayya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin gwamnonin da suka halarci zaman a Abuja

Gwamnonin da suka halarci wannan taro sun haɗa da, Bala Mohammed na Bauchi, Seyi Makinde na Oyo, Godwin Obaseki Edo, da Agbu Kefas na jihar Taraba.

Sauran sun haɗa da Dauda Lawal na Zamfara, Caleb Mutfwang na Filato da kuma mataimakan gwamnonin Enugu da Delta, Ifeanyi Ossai da Monday John Onyeme, bi da bi.

Wane batu zasu tattauna a taron?

Gwamnonin za su duba halin da kasar ke ciki da nufin ba da shawarwarin da za su zamo mafita ga Gwamnatin Tarayya.

Haka nan an tattaro cewa gwamnonin za su kuma duba matsalar rashin tsaron ƙasar nan da halin da jam’iyyar PDP ke ciki a jihar Edo gabanin zaben gwamna mai zuwa a jihar.

Kara karanta wannan

Ana cikin tsadar rayuwa, gwamnan PDP zai ɗauki sabbin malamai 5,000 da ɗaruruwan ma'aikata

Amma a rahoton Channels tv, ta ce har kawo yanzu babu cikakken bayani ko wata sanarwa a hukumance kan ajendojin da gwamnonin zasu fi maida hankali a taron.

APC ta tantance ƴan takara 12 a Edo

A wani rahoton kuma Jam'iyyar APC ta tantance ƴan takarar gwamna 12 da zasu fafata a zaben fidda gwani a jihar Edo.

Kwamitin tantance yan takarar jihar Edo ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren tsare-tsaren APC ta ƙasa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262