Ku Yi Amfani Da Dukiyarku Ku Tsamo 'Yan Najeriya Daga Talauci, Kungiyar APC Ta Fadawa Atiku da Obi

Ku Yi Amfani Da Dukiyarku Ku Tsamo 'Yan Najeriya Daga Talauci, Kungiyar APC Ta Fadawa Atiku da Obi

  • Hadakar kungiyoyi masu goyon bayan jam'iyyar APC ta bayyana cewa Shugaban Najeriya Bola Tinbu yana da manufa mai kyau ga 'yan Najeriya
  • Farfesa Mohammed Kailani, shugaban gamayyar ya shawarci 'yan jam'iyyun adawa su bada gudunmawa su yi amfani da dukiyarsu don ceto 'yan Najeriya daga talauci
  • Kailani, har ila yau, ya yi kira ga 'yan Najeriya su bai wa shugaban kasan hadin kai da goyon baya domin ya samu ya cimma manufofinsa na alheri a gare su

FCT Abuja - Gamayyar kungiyoyi magoya bayan APC ta ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu na da kyakkyawar manufa ga Najeriya kuma ya kamata kowane dan kasa ya bada gudunmawa don cimma manufofinsa.

Sun kum yi kira ga jagororin jam'iyyun adawa da su yi amfani da dukiyarsu don tsamo 'yan Najeriya daga kangin talauci.

Kara karanta wannan

Kano: Dan Majalisar Tarayya a NNPP ya gwangwaje 'yan jam'iyyarsa da abin alkairi, ya fadi dalili

Kungiyar APC ta roki Atiku da Obi su taimakawa talakawa da ke fama da talauci
Kungiyar APC ta shawarci Atiku da Obi su ceto tsamo talakawan Najeriya daga kangin talauci. Hoto: Bola Tinubu, Peter Obi, Atiku Abubakar
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban kungiyar, Farfesa Mohammed Kailani, shi ne ya bayyana haka a taron manema labarai a Abuja.

Kailani, wanda ya nemi a goyawa shugaban kasar baya, ya kuma yi kira ga 'yan adawa da su bar shi ya gudanar da mulki su daina masa katsa-landan.

"Shugaban kasa na da manufofi na yakar duk wani abu da zai hana walwalar al'ummar kasar nan.
"Shugaba Bola Tinubu na da manufofi, tunani da kuma tsari mai kyau don kawo ingantacciyar rayuwa ga yan Najeriya," in ji shi.

Kungiyar APC ta shawarci 'yan adawa su kyalle Tinubu ya yi mulki

A cewar babban daraktan, dole a kyale shugaban ya fuskanci matsalolin 'yan Najeriya, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

"Ina shawartar duk shugabannin 'yan adawa da su fara mayar da hankali kan gyara matsalolin jam'iyyunsu.
"Su mayar da hankali don kawo tsarukan da za su taimaki mutane, su nemo mafita kan matsalolin gabansu kafin fitowa su bayar da shawara ga gwamnatin da ke tafiya cikin nasara.

Kara karanta wannan

"Kada ka kalla idan kana da hawan jini": Matashi ya bada shawara gabannin wasan Najeriya na karshe

"Yan adawa na karyar cewa suna yi wa Najeriya fatan alheri, musamman Peter Obi na jam'iyyar LP da ke da kusan dala tiriliyan guda a asusunsa, a bankin Fidelity.
"Shi ma, Alhaji Atiku Abubakar, da ke da kusan kwatankwacin hakan a fadin duniya, kudaden da za su iya taimakawa mutane don cire su daga talauci."

Zaben 2027: APC Ta Yi Martani Yayin da Atiku Ya Fara Tunanin Sake Takara

A wani rahoton, jam’iyyar APC ta yi watsi da shirin da aka bayyana na ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar PDP a zaɓen 2019 da 2023, Atiku Abubakar, na tsayawa takara a zaɓen 2027.

Daraktan yada labarai na jam’iyyar APC, Bala Ibrahim, a wata hira da jaridar The Punch, wacce aka buga a safiyar Alhamis, 4 ga watan Janairu, ya bayyana burin Atiku na 2027 a matsayin labarai mafi ban dariya na 2024.

Kara karanta wannan

AFCON: Shehu Sani ya bai wa mata hanyoyin kare mazajensu daga mutuwa yayin kallon kwallo

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164