Majalisar Wakilai Ta Ɗauki Muhimmin Mataki da Nufin Gyara Yadda Ake Zaɓe a Najeriya

Majalisar Wakilai Ta Ɗauki Muhimmin Mataki da Nufin Gyara Yadda Ake Zaɓe a Najeriya

  • Kudirin sake garambawul a kundin dokokin zaben Najeriya 2022 ya tsallaka zuwa karatu na biyu a majalisar wakilan tarayya
  • Majalisar ta amince da kudirin a zaman ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu, 2024 bayan ɗan majalisa daga jihar Delta ya gabatar
  • Daga cikin abinda ake yunƙurin gyarawa har da batun tura sakamakon zaben ta intanet da kuma kunshin bayanan masu kaɗa kuri'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Majalisar wakilan tarayya ta amince da kudirin garambawul a kundin dokokin zaɓen Najeriya zuwa karatu na biyu, ranar Laraba, 7 ga watan Fabrairu.

Kudirin mai taken, "kudirin neman yi wa kundin dokokin zabe 2022 garambawul da sauran batutuwa masu alaka da haka," ya tsallake karatu na ɗaya zuwa na biyu, Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Matsalar tsaro: Birnin tarayya Abuja na fuskantar babbar barazana, majalisar dattawa ta magantu

Majalisar wakilan tarayya.
Kudirin Yi Wa Dokar Zabe Garambawul Ta Tsallaka Zuwa Karatu Na Biyu a Majalisa Hoto: HouseNGR
Asali: Twitter

Mamba mai wakiltar mazaɓar Ughelli ta Arewa/Ughelli ta Kudu/Udu daga jihar Delta, Mista Francis Waive, ne ya ɗauki nauyin gabatar da kudirin a zauren majalisa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa wannan kwaskwarima da za a yi wa kundin zai ba da damar buɗe hanyar, "tura sakamakon zabe ta intanet wanda zai bunkasa demokuraɗiyya ta ƙasar nan."

Da yake gabatar da kudirin a zauren majalisar wakilai, Mista Waive ya nuna damuwa kan gibin da ke akwai a kundin dokokin zaɓen kasar nan na 2022.

Ya kuma yi kira da a riƙa sake nazari kan kundin bayanan masu kaɗa kuri'a duk bayan shekara 10.

"Nazari kan rajistar masu kada kuri'a a kowane shekara 10 zai zama kyakkyawan mafari," in ji shi.

Meyasa za a yi wa dokar zaɓe gyara bayan amfani da ita sau 1 tal?

Kara karanta wannan

Tsadar rayuwa: Sabuwar zanga-zanga ta ɓarke a jihar Arewa, an yi wa mataimakin gwamna ihu

Waive ya ce gyaran dokar zabe ya zama dole idan aka yi la’akari da dimbin korafe-ƙorafe da ke tattare da babban zaben 2023 da ya gabata.

Ya ce majalisar tarayya ta kafa dokar ne domin tabbatar da sahihin zabe da kuma tabbatar da cewa duk sakamakon da ya fito bayan kammala jefa ƙuri'a zai zama karɓaɓɓe.

A cewarsa, bayan fara amfani da dokar a zaben 2023, akwai bukatar a gyara wasu kura-kurai da suka bayyana da kuma shirya tunkarar babban zaɓe na gaba, The Nation ta rahoto.

Majalisar datta ta sauya tunani

A wani rahoton Majalisar dattawa ta canza shawara bayan manyan hafsoshin tsaro sun bayyana a gabanta yau Laraba a Abuja.

Jim kaɗan bayan ta basu damar shiga zauren, majalisar ta ɗage zaman sauraron ƙarin haske daga bakinsu, kana ta aike da gayyata ga NSA da wasu ministoci.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262