Allahu Akbar: Gwamnan Arewa Ya Ayyana Hutun Kwana 1 a Jiharsa, Ya Kawo Dalili Mai Ƙarfi
- Gwamna Mala Buni ya ayyana hutun kwana ɗaya domin girmama marigayi tsohon gwamnan Yobe, Bukar Abba Ibrahim
- A wata sanarwa da kakakin gwamnan ya fitar, ya ce al'ummar jihar za su yi amfani da ranar domin yi wa marigayin addu'ar uku
- Buni da iyalan marigayin suna zaman makoki da karɓan gaisuwa a gidan gwamnati da ke Damaturu
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Yobe - Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya ayyana ranar Laraba 7 ga watan Fabrairu, 2024, a matsayin ranar hutu domin karrama tsohon gwamnan jihar, Sanata Bukar Abba Ibrahim.
Jaridar The Nation ta tattaro cewa gwamnan ya ba da hutun kwana ɗaya ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Yobe, Mamman Mohammed, ya fitar.
Haka nan mutanen Yobe za su kuma yi amfani da wannan rana da babu aiki wajen yin addu'ar uku ga marigayi tsohon gwamnan jihar, Bukar Abba Ibrahim.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Buni ya bukaci ‘yan jihar Yobe da su yi amfani da ranar domin yin addu’o’in girmama tsohon shugaban su da Allah ya yi wa rasuwa a kasar Saudiyya.
Idan baku manta ba, Legit Hausa ta kawo muku rahoton cewa tsohon gwamnan jihar Yobe ya rasu ranar Lahadi, 4 ga watan Fabrairu, 2024 a ƙasa mai tsarki.
Za a yi addu'ar uku a gidan gwamnatin jihar Yobe
Sanarwar ta ƙara da bayanin cewa za a gudanar da addu'ar uku ne a masallacin gidan gwamnati da ke Damaturu, babban birnin jihar Yobe a Arewa maso Gabas.
Bayanai sun nuna cewa tun bayan rasuwar tsohon gwamnan, mutane daga ciki da wajen jihar ke zuwa ta'aziyya a gidan gwamnatin, Daily Post ta ruwaito.
Gwamna Buni tare da jami’an gwamnati da iyalan marigayin, sun yi ta amsar gaisuwa da ta'aziyyar jama’a a gidan gwamnati da ke Damaturu.
Sanata Bukar Abba Ibrahim, bayan doguwar jinya ya rasu a kasar Saudiyya a ranar Lahadin da ta gabata, inda kuma aka binne shi washe gari.
Gwamnatin Kebbi ta kulle makarantun kuɗi 2
A wani rahoton na daban Wasu manyan makarantun gaba da sakandire na kuɗi sun shiga matsala a jihar Kebbi bisa rashin biyan haƙƙin gwamnati.
Gwamnatin Kebbi karkashin Gwamna Nasir Idris ta sanar da kulle makarantun guda biyu har sai sun biya kuɗaɗen da ake binsu.
Asali: Legit.ng