Fadar Shugaban Kasa Ta Sake Yin Martani Mai Zafi Ga Atiku Kan Abu 1 Tak

Fadar Shugaban Kasa Ta Sake Yin Martani Mai Zafi Ga Atiku Kan Abu 1 Tak

  • Fadar shugaban ƙasa ta mayar da martani ga Atiku Abubakar da ƙorafe-ƙorafen jam’iyyar PDP kan halin da ƙasar nan ke ciki
  • Bayo Onanuga ya jaddada cewa Tinubu ya mayar da hankali ne wajen gyara Najeriya da farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar nan wanda hakan zai ɗauki lokaci
  • Jigon na APC ya ce Atiku ya samu sabon aiki na sukar gwamnatin Tinubu tun bayan da ya kasa samun shugabancin ƙasar nan a zaɓen 2023

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

A daidai lokacin da hauhawar farashin kayayyaki da ƙarancin abinci ke ƙara taɓarɓarewa, fadar shugaban ƙasa ta ce ƴan Najeriya sun fi samun ƙarancin tsadar rayuwa a Afirika.

A ranar Lahadi, 4 ga watan Fabrairu, fadar shugaban ƙasar ta yi iƙirarin cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta mayar da hankali ne kan warware matsalolin tattalin arziƙi da tsaro da Najeriya ke fuskanta.

Kara karanta wannan

An yi rashi: Babban shugaban kasa a nahiyar Afirika ya rasu, bayanai sun fito

Fadar shugaban kasa ta yi wa Atiku martani
Fadar shugaban kasa ta yi martani kan kalaman Atiku Abubakar Hoto: Atiku Abubakar, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Ta kuma yi nuni da cewa sauye-sauyen da Tinubu ya yi za su haifar da wahalhalu na wani ɗan lokaci amma za su ci moriyarsu a nan gaba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayo Onanuga, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, ya bayyana hakan ne a cikin wani martani da ya yi kan Atiku Abubakar a shafinsa na X

Meyasa aka yi wa Atiku martani?

Martanin Onanuga ya biyo bayan zargin da Atiku ya yi na cewa manufofin tattalin arziki na Tinubu na haifar da raɗaɗi da kuma haddasa yanke ƙauna a tsakanin ƴan Najeriya.

Wani ɓangare na rubutun Onanuga na cewa:

"Tabbas Alhaji Atiku Abubakar ya samu wani sabon aikin da zai riƙa yi, bayan da ya kasa cimma daɗaɗɗen burinsa na zama shugaban Najeriya. Yana ƙara tabbatar da kansa a matsayin babban ɗan adawa ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatinsa.

Kara karanta wannan

"Zaka rasa aikinka": Ooni na Ife ya gayawa shugaban EFCC, ya fadi dalili

"Sai dai kuma mun lura cewa tsohon mataimakin shugaban ƙasar, kamar yadda yake yi a siyasance, bai ƙware a kan hakan ba, inda yake faɗin abubuwan da ba haka suke ba kan tattalin arziƙinmu da sauran abubuwan da suka shafi al’umma.

Maƙarƙashiya Kan Gwamnatin Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƙungiyar FNPP ta bankaɗo wata sabuwar maƙarƙashiya da ake ƙullawa a kan gwamnatin Shugaba Tinubu.

Ƙungiyar ta bayyana cewa ana shirya maƙarƙashiyar ne domin ganin gwamnatin ta kasa cimma manufofinta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng