Abin Da Yasa Kano, Jigawa Ba Su Fama Da Matsalar 'Yan Bindiga: Shehu Sani Ya Magantu
- Shehu Sani, tsohon sanata, ya yi bayanin cewa za a iya magance matsalar tsaron Najeriya akalla cikin hanyoyi hudu
- Tsohon dan majalisar ya yi bayanin cewa daya cikin hanyoyin da suka fi dacewa a yi yaki da rashin tsaro shine gwamnoni su kashe kudaden da ake turawa jihohinsu ta hanyoyin da suka dace
- Sani ya yi mamakin abin da yasa ba a samu ta'addanci ko 'yan fashin daji ba a jihohi kamar Kano da Jigawa
Aminu Ibrahim ya shafe fiye da shekaru 5 yana kawo rahotanni kan siyasa, al'amuran yau da kulum, da zabe
Kaduna - Shehu Sani, tsohon sanatan wanda ya wakilci Kaduna ta Tsakiya a majalisa ta takwas, ya bada shawarwari hudu ta yadda za a yi yaki da ta'addanci, 'yan bindiga da masu garkuwa a arewacin kasar.
Da ya ke magana a zauren 'space' da Legit.ng ta yi a manhajar x a ranar Alhamis, 1 ga watan Fabrairu, mai rajjin kare hakkin bil adaman ya yi tambayar mai yasa ba a samun ta'addanci a wasu jihohin arewa, musamman Kano da Jigawa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon sanatan ya ce saboda gwamonin jihohin, tsawon lokaci, suna daukan batun tsaron rayuka da dukiyoyin al'umma da muhimmanci, kuma suna kashe kudin tsaro da ake tura musu yadda ya dace.
A cewar tsohon sanatan, 'Yan Najeriya ba za su jinjinawa Shugaba Bola Tinubu ba saboda kokari; mutane na son a kawar da ta'addanci, 'yan bindiga da garkuwa da mutane baki daya ne, ya kara da cewa abin na bazuwa daga arewa zuwa kudu.
Hanyoyi hudu da za a magance rashin tsaro a Najeriya, Shehu Sani
Ya kara da cewa hanya mafi dacewa don magance matsalar shine a dena tura kudi kawai. Maimakon hakan, a saka ido kan yadda ake kashe kudin da aka ware don tsaro.
Kuma, Sani ya ce a yi amfani da na'ura da mutane wurin tattara bayanan sirri don yaki da rashin tsaro, ya kara da cewa a duba me yasa kasashe kamar Benin da Jamhuriyar Nijar ba su fama da irin matsalar da Najeriya ke fama da shi.
Dan siyasan haifafan jihar Kaduna ya kuma bada shawarar cewa idan ba a kirkiri 'yan sandan jihohi ba, toh, a rika tura 'yan sandan tarayya zuwa jihohinsu na anihi saboda za su fi sanin lungu da sakuna kuma mutanensu za su yarda da su.
Sani ya ce:
"Akwai labarin nasarori a Najeriya; me yasa babu 'yan bindiga a Kano? Me yasa babu 'yan ta'adda a jihar Kano? Kuma wadannan jihohin arewa maso yamma ne. Saboda gwamnonin ba su wasa da batun tsaro.
"Tun daga Kwankwaso zuwa Ganduje da yanzu Abba, ba su wasa da tsaro. Kamata ya yi a kashe kudin tsaro kan tsaro, ba rabawa magoya baya ba, 'yan daban siyasa da harkokin siyasa. Idan munyi hakan, za mu dace."
Asali: Legit.ng