Hukumar INEC Ta Bayyana Jami'yyar da Ta Yi Nasara a Zaben Maye Gurbin Gbajabiamila, an Fadi Kuri'u

Hukumar INEC Ta Bayyana Jami'yyar da Ta Yi Nasara a Zaben Maye Gurbin Gbajabiamila, an Fadi Kuri'u

  • An gama tattara sakamakon zaben mazabar Surulere a jihar Legas a yau Asabar 3 ga watan Faburairu
  • Hukumar zabe ta ayyana Fuad Laguda na jami'yyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben da aka gudanar
  • Laguda, tsohon shugaban jam'iyyar APC a Surulere zai maye gurbin shugaban ma'aikata, Femi Gbajabiamila

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar da wanda ya yi nasara a zaben cike gurbi da aka gudanar a jihar Legas.

Hukumar ta bayyana Fuad Laguda na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben mazabar Surulere a Majalisar Wakilai.

INEC ta bayyana sakamakon zaben Surulere a Legas
Hukumar INEC Ta Bayyana Jami'yyar da Ta Yi Nasara a Zaben Maye Gurbi a Legas. Hoto: Femi Gbajabiamila, Fuad Laguda.
Asali: Twitter

Waye INEC ta sanar wanda ya lashe zaben?

Kara karanta wannan

INEC ta sanar da ɗan tsohon sifetan 'yan sanda wanda ya lashe zaben Majalisa, bayanai sun fito

Yayin da yake bayyana sakamakon zaben, Farfesa Simeon Adebayo ya ce Fuad Laguda ya yi nasara da kuri'u 11,203, cewar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Laguda, tsohon shugaban jam'iyyar APC a karamar hukumar Surulere zai maye gurbin Femi Gbajabiamila a Majalisar.

Gbajabiamila ya bar kujerar ce bayan Shugaba Tinubu ya nada shi a matsayin shugaban ma'aikatan Gwamnatin Tarayya, cewar The Nation.

Yadda INEC ta sanar da yawan kuri'un 'yan takara

Ga yadda zaben ya kasance:

ADC - 40

APC - 11,203

APGA - 6

APM - 7

APP - 4

LP - 240

NNPP - 8

PDP - 278

SDP - 2

YPP - 9

ZLP - 4

Har ila yau, Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta sanar da sakamakon zaben cike gurbi a jihar Kano.

INEC ta fitar da sanarwar ce kan sakamakon zaben cike gurbi a mazabar Rimin Gado/Tofa a Majalisar jihar Kano.

Kara karanta wannan

Kano: Jami'yyar NNPP ta kifar da APC a zaben cike gurbi a wata mazaba a jihar, bayanai sun fito

Wannan na zuwa ne bayan soke zaben mazabar Kunchi/Tsanyawa da hukumar zabe ta yi saboda rikici.

Ehindero ya lashe zaben Akoko a ondo

Kun ji cewa Hukumar zabe ta INEC ta sanar da wanda ya lashe zabe a mazabar Akoko da ke jihar Ondo a Majalisar Tarayya.

Hukumar ta ayyana Ifeoluwa Ehindero na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya yi nasara a zaben.

Faresa Johnson Fasinmirin shi ya ayyana Ehindero a matsayin wanda ya lashe zaben bayan kammala tattara sakamakon zaben.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.