Zaben Cike Gurbi: Sojoji Sun Kama Shugaban Matasa Tare da Wani Mutum 1 a Ebonyi
- Rahotanni sun bayyana cewa sojoji sun kama shugaban matasa a karamar hukumar Afikpo da ke jhar Ebonyi yayin da ake zaben cike gurbi
- Haka zalika sojojin sun yi awon gaba da wani Inya Kenneth bayan kai sumame a Kasuwar Afikpo misalin karfe 1 na ranar Asabar
- Dan takarar jam'iyyar APGA ya yi Allah wadai kan yadda 'yan siyasa ke amfani da sojoji wajen cin zarafin al'umma a Ebonyi ta Kudu
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Jihar Ebonyi - A ranar Asabar ne sojoji suka kama wasu mutane biyu a karamar hukumar Afikpo yayin zaben maye gurbin Sanatan Ebonyi ta Kudu.
Daya daga cikin wadanda aka kama shine Obila Ojo, shugaban matasa a yankin, wanda aka kama shi da daddare a gidansa.
Sojoji sun kuma kai sumame Kasuwar Afikpo
An sake shi ne bayan sa’o’i da dama biyo bayan matsin lamba da dan takarar jam’iyyar All Progressive Grand Alliance (APGA), Ifeanyi Eleje ya yi wa sojojin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun kuma kai sumame a mazabar sabuwar Kasuwar Afikpo da misalin karfe 1:00 na rana inda suka kama wani Inya Kenneth, The Nation ta ruwaito.
Matarsa, Margaret Inya, ta ce wani dan adawa ne ya zo da jami’an sojoji ya nuna mijinta inda yake zaune da abokansa ya ce su kama shi.
Sojoji sun zama barazana ga dimokuradiyya - Eleje
Ta ce sojojin sun ajiye mijin nata a kasa cikin rana na sama da awa daya kafin su saka shi a motarsu suka yi awon gaba da shi.
Eleje ya yi Allah wadai da faruwar lamarin inda ya kara da cewa jami’an sojin ba su bayar da wani dalili na kamen ba.
Ya ce jami’an tsaro su ne babbar barazana ga dimokuradiyya, yana mai zargin cewa suna hada baki da ‘yan siyasa domin rushe zabin al’umma.
Ba a iya samun jin ta bakin hukumomin soji a jihar kan wannan lamari ba har zuwa kammala rubuta rahoton.
PDP ta yi zargin ana sayen kuri'u a Kaduna
A wani labarin, wakilin jam'iyyar PDP a rumfar zaben 009 da ke Barnawa, Kaduna ta Kudu a jihar Kaduna, ya yi zargin cewa ana hada kai da jam'an tsaro ana sayen kuri'u.
Ya ruwaito cewa jami'an tsaron na kallo ana sayen kuri'u a bainar jama'a ba tare da daukar mataki ba, wanda hakan barazana ne ga dimokuradiyya.
Asali: Legit.ng